Zaɓen Shugaban Ƙasa zai gudana 20 ga Fabrairu, 2027

INEC Ta Fitar da Jadawalin Zaɓukan 2027

Hukumar zaɓen Nijeriya (INEC) ta sanar da jadawalin zaɓukan shekarar 2027, inda ta bayyana cewa za a gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a ranar Asabar, 20 ga Fabrairu, 2027. TRT Hausa

A cewar jadawalin, zaɓen gwamnonin jihohi da na Majalisun Dokoki na Jihohi zai biyo bayan makonni biyu, wato ranar Asabar, 6 ga Maris, 2027, wanda zai zo daidai da tsakiyar watan azumin Ramadan. TRT Hausa

INEC ta ce yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa zai fara daga 18 ga Nuwamban 2026 zuwa 19 ga Fabrairun 2027, yayin da na gwamna da ‘yan Majalisar Jiha zai fara 15 ga Disamban 2026 ya ƙare 5 ga Maris, 2027. TRT Hausa

Hukumar ta kuma bayyana cewa rijistar masu zaɓe akai-akai (CVR) za ta fara a Afrilun 2026 kuma ta ƙare a Janairun 2027, domin bai wa ‘yan ƙasa damar yin rijista ko sabunta bayanansu. TRT Hausa

Jam’iyyun siyasa za su gudanar da zaɓen fidda gwani daga 1 ga Yuli zuwa 30 ga Satumban 2026, sannan su miƙa jerin ‘yan takararsu tsakanin 1 ga Oktoba zuwa 31 ga Oktoban 2026, yayin da za a fitar da jerin ‘yan takara na ƙarshe a 15 ga Nuwamban 2026. TRT Hausa

INEC ta kuma nemi naira biliyan 873 domin gudanar da zaɓukan 2027, inda ta bayyana cewa kuɗaɗen sun haɗa da na ayyukan zaɓe, gudanarwa, fasaha, da manyan kayayyaki da za a yi amfani da su. TRT Hausa

Shugaban INEC, Joash Amupitan, ya ce wannan kasafi ya bambanta da na shekarar 2026 wanda ya kai naira biliyan 171, kuma ‘yan majalisa sun ce za su yi cikakken bincike kafin amincewa da shi. TRT Hausa

Haka kuma, an bayyana cewa kimanin matasa masu yi wa ƙasa hidima 450,000 ne ake sa ran za a tura ayyukan zaɓe, inda kowane zai karɓi naira 127,000 tare da ƙarin alawus na abinci da horaswa. TRT Hausa

 
 
 
 
 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#