Operation Hadin Kai ta ƙara ƙaimi a yaƙin da Boko Haram da ISWAP

Sojojin Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda 30, sun dawo da ‘yan gudun hijira 700

Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta ce dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun kawar da fiye da ‘yan ta’adda 30 tare da taimaka wa fiye da ‘yan gudun hijira ‘yan Nijeriya 700 komawa gida cikin makon da ya gabata, sakamakon ƙara ƙaimi a ayyukan yaƙi da ta’addanci a arewa-maso-gabashin ƙasar. TRT Hausa

Daraktan Harkokin Watsa Labarai na Tsaro, Maj-Gen Michael Onoja, ya ce nasarorin sun samo asali ne daga farmaki bisa bayanan sirri kan Boko Haram, ISWAP da JAS, tare da haɗin gwiwar sojin sama da ƙungiyoyin tsaro na yankin. TRT Hausa

A yankin Timbuktu Triangle kusa da Kimba a ƙaramar hukumar Damboa ta Jihar Borno, sojoji sun kashe fiye da ‘yan ta’adda 20 ciki har da wani kwamanda da ake kira Julaibib, tare da rusa manyan wuraren tsare ‘yan ta’adda guda uku da ceto mutane 70. TRT Hausa

Haka kuma an samu ƙarin nasarori a Gwoza (Borno), Hong da Mubi North (Adamawa), inda aka kama masu satar mutane, aka ceto waɗanda aka sace, tare da ƙwato makamai da kayan soji. TRT Hausa

Rundunar ta kuma taimaka wajen dawo da rukuni na biyu na kusan ‘yan gudun hijira ‘yan Nijeriya 700 daga Kamaru ta iyakar Banki a ƙaramar hukumar Bama ta Jihar Borno, tare da samar da cikakken tsaro a duk tsawon aikin. TRT Hausa

 
 
 
 
 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#