An kai harin asubahi a gidan fasto a Kauru

‘Yanbindiga sun kashe mutane uku, sun sace faston Katolika a Kaduna

‘Yanbindiga sun kashe mutane uku tare da sace wani faston Katolika da wasu mutane yayin wani harin da suka kai da sanyin safiya a gidan faston a Ƙaramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna, kamar yadda majiyoyin coci da ‘yan sanda suka bayyana a ranar Lahadi. TRT Hausa

Cocin Katolika reshen Kafanchan ta ce faston da aka sace shi ne Nathaniel Asuwaye na cocin Holy Trinity Catholic Church da ke Karku, inda ta ƙara da cewa mutane 10 aka sace, yayin da harin ya fara da misalin ƙarfe 3:20 na safe. TRT Hausa

Sai dai rundunar ‘yansandan Kaduna ta ce mutum biyar ne aka sace gaba ɗaya, kuma mutane ukun da suka mutu jami’an tsaro ne bayan musayar wuta da ‘yanbindigar, inda sojoji biyu da ɗan sanda ɗaya suka rasu. TRT Hausa

Fafaroma Leo ya nuna alhini da goyon baya ga mutanen da hare-haren ‘yanbindiga ke shafa a Nijeriya, yana mai kira ga hukumomi da su ƙara ƙoƙari wajen tabbatar da tsaro da kare rayukan ‘yan ƙasa. TRT Hausa

 
 
 

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#