Jakar wani muhimmin abin amfani ce a rayuwar yau da kullum, inda ake amfani da ita wajen ɗaukar kayayyaki daban-daban, Sai dai kuma, tana ɗauke da tunane-tunane masu raɗaɗi na wasu munanan abubuwan da suka faru a tarihi.

Tashe da abubuwan tunawa masu ciwo da suka faru game da mashahuriyar jakar ‘Ghana Must Go’

Daga kasuwannin da ke cike da jama’a na birnin Accra zuwa manyan titunan Hong Kong masu yawan zirga-zirga, shahararriyar jakar nan mai ratsin launukan ja, fari da shuɗi, wadda aka fi sani da “Ghana Must Go”, ta ratsa iyakokin ƙasashe da kuma al’ummu daban-daban.

Jakar da mutane ke amfani da ita a rayuwarsu ta yau da kullum wajen ɗaukar kayayyaki daban-daban, tun daga tufafi da kayan amfanin gida zuwa abinci, tana kuma ɗauke da munanan abubuwan tarihi na korar jama’a da tilasta musu barin muhallansu.

“Ghana Must Go! Ga ta nan, ku zo ku saya. Tana da kyau, tana da kyau,” in ji Agnes Ambomah, tana tallata jakunkunanta cikin salon waƙa daga rumfarta da ke gefen titi a babban birnin Ghana, Accra.

“Wannan kalar ja ɗin na da inganci sosai. Wannan kuma ta asali ce,” in ji ta, yayin da take ɗaga ɗaya daga cikin jakunkunan domin nuna wa wani kwastoma.

A yanzu tana da shekaru 38, don haka ta yi ƙanƙanta sosai a lokacin da abubuwan da suka sa aka sanya wa jakar wannan suna mai ɗauke da mummunan tarihi suka faru, kuma ba ta iya tunawa da su.

Sai dai a wajen Bashiru Tahiru mai shekaru 70, ganin wannan jaka na dawo masa da wasu abubuwan da suka faru a baya waɗanda da ma ba ya son sake tunawa da su.

“Jaka ce da ke kawo sa’a mara kyau. Ba na amfani da ita,” Tahiru ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP daga shagon sayar da tufafinsa da ke babbar kasuwar Makola a birnin Accra.

Tahiru na cikin kimanin ’yan Ghana miliyan ɗaya da aka tilasta wa barin Najeriya a farkon shekarun 1980, a lokacin da gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin korar baƙin haure da ba su da takardun zama a ƙasar.

Abubuwan tunawa

A lokacin da yake aiki a matsayin ma’aikacin tashar jiragen ruwa a Legas, ya tuna yadda ya tattara kayansa a ɗaya daga cikin jakunkunansa masu ratsin launukan, yayin da yake shirin barin ƙasar.

Ya ce yana tsoron mutane su gan shi a kan titi yana ɗauke da jakar, domin a lokacin tuni ta zama wata alama da ake danganta wa bakin hauren da ake korar su daga ƙasar.

Bayan shekaru da dama, rikicin nuna ƙiyayya ga baƙin haure da ya sake barkewa a Afirka ta Kudu a bana, ciki har da hare-haren da aka kai kan ’yan Ghana da ke zaune a ƙasar, ya dawo masa da waɗancan abubuwan tunawa.

“Wannan jakar tana tuna min da irin wahalhalun da na sha a Najeriya,” ya shaida wa AFP da harshen Pidgin na Najeriya.

Sanye da riga mai ratsin baƙi da fari da hular kai baƙa, Tahiru ya tuna yadda ya bar Najeriya a cikin ɗaya daga cikin jiragen dakon kaya da gwamnatin Ghana ta shirya domin kwashe ’yan ƙasarta daga Najeriya.

A wannan karon kuwa, Ghana da Najeriya sun kasance a ɓangare guda, inda suka jagoranci ƙoƙarin diflomasiyya na nuna adawa da matakan Pretoria, tare da shirya jiragen sama domin kwashe ’yan ƙasarsu daga Afirka ta Kudu.

Rikicin kyamar baki

Rikicin ya haifar da muhawara a kafafen sada zumunta game da ma’anar da wannan jaka ke ɗauke da ita.

Wasu ’yan Afirka ta Kudu sun bayyana cewa asalin jakar Ghana Must Go abin tunawa ne da cewa kowace ƙasa, kamar yadda Najeriya ta yi a wancan lokaci, haka Afirka ta Kudu a yanzu, tana da ’yancin cewa, “Ya isa haka.”

Sai dai ba a ga waɗannan shahararrun jakunkuna a cikin kayayyakin da mutanen da ke komawa Ghana da Najeriya suka tafi da su ba, saboda wasu kamfanonin jiragen sama sun hana a karbi jakunkunan domin shiga jirgi, sai dai idan an saka su cikin akwati mai tauri. Kamfanonin sun bayyana cewa matakin ya biyo bayan yawan lalacewar na’urorin jigilar kaya a filayen jiragen sama da jakunkunan ke haddasawa.

Sai dai an ga waɗannan jakunkuna masu ratsin launuka ana jigilar su a kan hanya, yayin da baƙin haure ke tserewa daga Afirka ta Kudu zuwa Malawi, Zimbabwe da Mozambique.

Tarihin wannan jaka ya samo asali ne daga Hong Kong a shekarun 1960, a lokacin da tattalin arzikin birnin ke samun bunƙasa.

Ana danganta nasarar mayar da wannan yadi, wanda ake samo shi daga Taiwan da Japan, zuwa jakunkuna masu ƙarfi da kuma hana ruwa shiga da wani ƙwararren mai sana’a mai suna Lee Wah, wanda ya kafa kamfanin Wah Ngai Canvas.

Yayin da China ta fara buɗe ƙofofinta ga duniya sannu a hankali a shekarun 1970, dubban mazauna Hong Kong sun yi amfani da waɗannan jakunkuna wajen jigilar kayayyaki yayin da suke ziyartar ’yan uwansu da ke yankunan babban yankin China.

Har yanzu ana kallon waɗannan jakunkuna a matsayin wata alama da ke wakiltar juriya da ƙarfin halin mutanen Hong Kong, duk da cewa an mayar da yawancin ayyukan ƙera su zuwa babban yankin China.

“Ƙarfin ruhin Hong Kong shi ne ruhin da ba ya karaya... Yana nufin cewa komai wahalar rayuwa, mutum zai iya jurewa har ya shawo kanta,” ɗan Lee, wanda ya karɓi ragamar gudanar da kasuwancin iyalinsu amma ba ya son fitowa fili, ya shaida wa AFP.

Jakunkuna cike da ‘so da kauna’

A Yammacin Afirka, wannan jaka wadda a da ake danganta ta da wulaƙanci sakamakon korar mutane da kuma talauci, ta zama wani muhimmin abin amfani a rayuwar yau da kullum tsawon shekaru.

“Ta zama jaka ta amfanin yau da kullum,” in ji Kweku Darko Ankrah, wani masanin tarihi a Jami’ar Ghana. “Ma’anar mummunan zato da ake dangantawa da ƙaura daga ƙasa zuwa wata ba ta nan kamar yadda take a da.”

Haka kuma, masu fasaha da masu zane-zane sun ƙara nuna sha’awarsu ga wannan yadi da ake ƙera jakar da shi.

Wani ɗan ƙasar Ghana mai zane-zane, Abdur Rahman Muhammad, mai shekaru 38, yana amfani da zanen ratsin jakar a matsayin wani salo na baya da yake maimaitawa yayin zana hotunan mutane.

“A cikin ayyukana, wannan jaka ta zama alamar juriya, fata da kuma ƙoƙarin cim ma burin rayuwa,” in ji shi a ɗakin aikinsa da ke birnin Accra.

‘Hanyata ta nuna so da kauna’

A shekarar 2007, shahararren kamfanin ƙera kayan alatu na Louis Vuitton ya fitar da nasa nau’in wannan jaka, lamarin da ya jawo zarge-zargen yin amfani da al’adun wasu al’umma ba tare da girmama su ba, da kuma rashin nuna kulawa ga alaƙar jakar da tarihin korar jama’a daga ƙasashensu

Sai dai a cewar Ankrah, wannan mataki ya kuma nuna “yadda matsayin jakar ya sauya daga kasancewa kayan talakawa zuwa kayan masu matsakaicin ƙarfi, har ma da masu hannu da shuni.”

Haka kuma, jakar ta shahara a tsakanin ma’aikatan gida ’yan ƙasashen waje da ke aiki a Hong Kong, waɗanda ke cikin manyan al’ummomi ma’aikata a wannan cibiyar harkokin kuɗi ta duniya.

A duk ranar Lahadi, wato ranar hutunsu ta mako, Jenalyn Polinar da sauran ’yan uwanta ’yan ƙasar Philippines kan taru a kan titunan Hong Kong domin cika jakunkunan da takalma, tufafi, taliyar noodles da kayan tsafta, waɗanda za a aika zuwa ƙauyukansu na asali.

“Wannan ita ce hanyata ta nuna musu ƙaunata,” Polinar mai shekaru 39 ta shaida wa AFP.

Nilda Bendo, mai shekaru 56, ta shafe shekaru 20 tana amfani da waɗannan jakunkuna wajen aika wa iyalanta kayayyaki da kyaututtuka.

“Jaka ce mai sauƙin ƙira, amma tana iya ɗaukar abubuwa da yawa a cikinta,” in ji ta.

“Tana cike da kayayyaki,” in ji ta, tana mai cewa duk lokacin da jakar ta isa wurin iyalanta, ba sa iya jira su buɗe ta domin ganin abin da ke cikin ta.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: AFP

#