Matakin wani ƙari ne ga jerin sauya sheƙa na dakaru da jami'an siyasan RSF a cikin 'yan watannin nan.

Kwamandan RSF da dakarunsa sun sauya sheka zuwa rundunar sojin Sudan

Wani kwamandan RSF ya fice daga cikin rundunar inda ya koma cikin sojojin Sudan tare da dakarun da ke ƙarƙashin ikonsa ranar Laraba, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya ruwaito.

Mishal Abdelrahman, kawamnadan ƙungiyoyi na 27 da na 28 na dakarun RSF, ya bayyana sauya sheƙarsa a gaban jami’an soji da na leƙen asiri.

Ya ce dakaraunsa sun koma cikin sojojin ne bisa raɗin kansu kuma sun shirya domin yaƙi kafaɗa da kafaɗa da dakarun sojin. SUNA bai fayyace adadin dakarun ba.

Matakin ya kasance ƙari ga jerin sauya sheƙa daga dakaru da jami’an RSF a cikin ‘yan watannin nan. A ranar 2 ga watan Nuwamba, sojin ya ce wata tawagar ta daban ta miƙa wuya ga rundunarsa ta 4 ta sojojin ƙasa a Damazin, babban birnin Jihar Blue Nile.

Ƙarfafa kariya

A wani ɓangaren na daban kuma, sojin ya ce tsarin tsaron sararin samaniyarsa ya kakkaɓo wani jirgi mara matuƙa a kudu maso yammacin Karnoy a North Darfur ranar Laraba da yamma.

A wata gajeruwar sanarwa, sojin ya bayyana jirgin saman a matsayin wani “jirgi mara matuƙa na musmaman na abokan gaba” ba tare da fayyane wanda ya sarrfa shi ba ko kuma samfurin sa.

Sudan ta kasance cikin rikici tun ranar 15 ga watan Afrilu na shekarar 2023, a lokacin da yaƙi ya ɓarke tsakanin sojin ƙasar da rundunar RSF bisa rashin jituwa game da shigar da mayaƙan RSF cikin sojin ƙasar.

Yaƙin ya kashe gomman dubban mutane tare da raba miliyoyin mutane da gidajensu da kuma haddasa lalata ababen more rayuwa na fararen hula da yawa, ciki har da asibitoci da kayayyakin jinya.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: AP

#