Hukumar ta ce an ɓoye kayayyakin ne a cikin wasu kwalaye 33 da aka bayyana a matsayin kayayyakin amfanin kai, waɗanda aka shigo da su cikin Kano ta jirgin saman Ethiopian Airlines da ya sauka a filin jirgin a ranar Laraba.
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Nijeriya (NAFDAC) ta ƙwace kwalaye 17 na wasu abubuwan sha, alluran sauya launin fata da na rage tsufa da ake zargin ba su da rajista a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke Jihar Kano.
Hukumar ta ce an ɓoye kayayyakin ne a cikin wasu kwalaye 33 da aka bayyana a matsayin kayayyakin amfanin kai, waɗanda aka shigo da su cikin Kano ta jirgin saman Ethiopian Airlines da ya sauka a filin jirgin a ranar Laraba.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, NAFDAC ta ce sashen kula da kayayyakin da ake shigowa da su ta tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama ne ya gano kayayyakin yayin wani bincike na haɗin gwiwa a cibiyar kamfanin Skyway Aviation Handling Company (SAHCO) da ke filin jirgin.
Hukumar ta ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa kayayyakin da ake zargin suna ƙarƙashin kulawarta ba su da lambobin rajistar NAFDAC.
Haka kuma, babu takardun izinin shigo da su da doka ta tanada, lamarin da ya haifar da damuwa kan halaccin shigo da su ƙasar.
Bayan gano kayayyakin, hukumar ta ce an dakatar da jigilar dukkan kwalayen, inda aka ajiye su a hannun Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS).
NAFDAC ta ƙara da cewa daga bisani ta gayyaci wanda ya shigo da kayayyakin domin yi masa tambayoyi, kuma ya bayar da bayani a matsayin wani ɓangare na binciken da ake gudanarwa.
Hukumar ta ce kayayyakin za su ci gaba da kasancewa a hannun Kwastam har sai an bayar da ƙarin umarnin da ya dace.
Sai dai NAFDAC ta yi gargaɗin cewa har yanzu ba a tabbatar da inganci da sahihancin kayayyakin da aka ƙwace ba.
Ta ce wannan samame na daga cikin ƙoƙarinta na ƙarfafa sa ido da tabbatar da bin ƙa'idoji a wuraren da ake shigar da kaya cikin Nijeriya, domin hana shigo da kayayyakin da ba su da rajista, marasa inganci ko kuma na jabu.
Hukumar ta jaddada cewa za ta ci gaba da tsaurara sa ido domin kare ’yan Nijeriya daga kayayyakin da ka iya cutar da su da kuma kiyaye lafiyar al’umma.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: NAFDAC Nigeria

