Hukumar ta ce yanayi na El Niño da ke gudana zai iya taɓarɓare yanayi na zafi da ƙura busasshe, lamarin da zai ƙara barazanar yaɗuwar cututtuka na numfashi da sauran cututtuka masu alaƙa da yanayi.
Hukumar Lafiya ta Ghana (GHS) ta yi gargaɗin yiwuwar samun yaɗuwar sanƙarau da gajiya na zafi da rashin ruwa a jiki yayin da Ghana ke shirin tunkarar lokacin hunturu.
Hukumar ta ce yanayi na El Niño da ke tafe zai iya samar da yanayi na zafi da rashin ruwa da yanayi mai ƙura mai ƙamari, inda zai ƙara barazanar yaɗuwar cututtuka na numfashi da sauran cututtuka masu alaƙa da yanayi.
A cikin wata sanarwa ta lafiyar al’umma da ta fitar ranar Laraba 18 ga watan Nuwamban 2026, hukumar GHS ta ce yanayi mai zafi da ake tsammani da tsawon lokaci na rashin ruwa da ƙarin yawan ƙura za su iya barazana ta lafiya ga mutane a sassan ƙasar.
Sanarwar, wadda Darakta Janar na Hukumar Lafiya ta Ghana, Dr Samuel Kaba Akoriyea, ya sanya wa hannu, ta kuma yi gargaɗi game da yiwuwar samun ruwan sama na bazata da ambaliya a sassan kudancin Ghana, tana mai kira ga al’ummomi su kasance cikin shiri kuma su ɗauki matakan kariya da suka dace.
Kazalika hukumar ta yi kira ga iyaye da malamai da sarakunan gargajiya da shugabannin addinai da ƙungiyoyi na al’umma da Ƙananan Hukumomi su zafafa wayar da kan jama’a game da barazana ta lafiya da kuma gabatar da matakai na kariya.
Ta bayyana lardunan Northern da Upper East da Upper West da Savannah da North East da Bono East a matsayin wuraren da ke buƙatar ƙarin wayar da kan jama’a saboda barazanar da suke fuskanta daga yanayin da ake dako.
Hukumar GHS ta ce yanayi na zafi mara ruwa da ke da ƙura da aka alaƙanta da hunturu da ke ƙaratowa zai iya ƙara barazanar kamuwa da cututtuka na numfashi da ɓullar sanƙarau.
Sai dai kuma ta gaggauta bayyana cewa El Niño ba ya nufin cewa dole sai an sami ɓullar cutar sanƙarau.
Hukumar ta ce shiri da wuri da kuma matakai na kariya suna da muhimmanci wajen rage yiwuwar haɗurar lafiya.
Gargaɗin na zuwa ne baya hasashen da Hukumar Hasashen yanayi ta Ghana (GMet) ta yi cewa za a samu wani yanayi da ya fi zafi da rashin ruwa da ƙura a cikin lokacin ranin da ke zuwa, wanda ake tsammanin za a yi daga ƙarshen watan Nuwamba zuwa watan Maris na 2027.
GMet ta kuma yi hasashen cewa matsin zafi zai iya kasancewa mafi yawa tsakanin watan Fabrairu zuwa Afrilun shekarar 2027, musamman a sassan arewacin ƙasar.
Hukumar GHS ta ce za ta ci gaba da sa ido kan lamarin da kuma ba da bayanai ga jama’a idan buƙatar hakan ta taso.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: AFP (Wire)

