A cewar jaridar Daily Trust, sanatoci sun bayyana matakin a matsayin “wani babban sauyi a tarihi” a ƙoƙarin Nijeriya na shawo kan matsalolin rashin tsaro, garkuwa da mutane, ta'addancin 'yan bindiga da sauran ƙalubalen tsaro da ke fuskantar ƙasar.
Majalisar Dattawan Nijeriya ta umarci magatakardar Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ya miƙa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kudirin kafa rundunonin 'yan sandan jihohi domin ya sanya masa hannu, bayan amincewar Majalisar Dokoki ta Ƙasa da kuma majalisun dokokin jihohi 36.
An cimma matsayar ne a ranar Laraba, bayan muhawara kan kudirin gyaran kundin tsarin mulkin Nijeriya na shida na shekarar 2026, wanda ke neman samar da damar kafa rundunonin 'yan sandan jihohi.
A cewar jaridar Daily Trust, sanatoci sun bayyana matakin a matsayin “wani babban sauyi a tarihi” a ƙoƙarin Nijeriya na shawo kan matsalolin rashin tsaro, garkuwa da mutane, ta'addancin 'yan bindiga da sauran ƙalubalen tsaro da ke fuskantar ƙasar.
Da yake jagorantar muhawarar, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulkin a watan Yuni da Yuli na 2026, bi da bi, inda suka samu rinjayen kashi biyu bisa uku na ƙuri'un da kundin tsarin mulki ya tanada.
Ya ƙara da cewa dukkan majalisun dokokin jihohi 36 sun amince da kudirin, wanda hakan ya cika sharuɗɗan sashe na tara na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999, wanda ya tanadi yadda za a yi wa kundin tsarin mulkin gyara.
Bayan tabbatar da cewa an cika dukkan sharuɗɗan da ake buƙata, Majalisar Dattawan ta umarci magatakardar Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ya miƙa kudirin ga Shugaba Tinubu domin ya sanya masa hannu.
Sanatocin sun kuma yaba wa Shugaban Ƙasar bisa goyon bayan da yake bai wa shirin kafa rundunonin 'yan sandan jihohi.
Sun kuma buƙace shi da ya miƙa kudirin dokar kula da ayyukan rundunonin 'yan sandan jihohi ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa domin ta yi nazari a kai.
Ana sa ran dokar da ake shirin samarwa za ta fayyace yadda rundunonin 'yan sandan jihohin za su gudanar da ayyukansu, da kuma yadda za su yi aiki tare da rundunar 'yan sandan tarayya.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kiraye-kirayen raba tsarin aikin 'yan sanda, domin kusantar da ayyukan tsaro ga al'ummomi da kuma ƙarfafa matakan magance barazanar tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: Nigerian Senate

