Tun a ranar 17 ga Fabrairu gwamnatin Gabon ta katse amfani da kafafen sada zumunta, ciki har da Facebook da TikTok, tana mai zargin cewa abubuwan da ake wallafawa a intanet suna haddasa rikici da rarrabuwar kawuna a cikin al’umma.

Gabon ta janye takunkumin amfani da kafafen sada zumunta bayan watanni takwas

Gabon ta dawo da damar amfani da kafafen sada zumunta, kamar yadda hukumar kula da harkokin yaɗa sadarwa ta ƙasar ta bayyana, bayan dakatar da su na tsawon watanni takwas, matakin da ya jawo suka mai yawa.

Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa ta Gabon (HAC) ta katse amfani da kafafen sada zumunta, ciki har da Facebook da TikTok, a ranar 17 ga Fabrairu, tana mai zargin cewa abubuwan da ake wallafawa a intanet suna haddasa rikici da rarrabuwar kawuna a cikin al’umma.

“HAC ta yanke shawarar ɗage dakatarwar da aka sanya wa kafafen sada zumunta,” in ji kakakin hukumar, Jean-Claude Franck Mendome, a cikin wata sanarwa da aka karanta a talabijin.

An rufe Facebook da TikTok, waɗanda su ne kafafen da aka fi amfani da su a ƙasar da ke tsakiyar Afirka, da kuma YouTube da Instagram. Sai dai an riƙa samun katsewar amfani da WhatsApp lokaci-lokaci.

Tsarin doka

Wasu mutane sun ci gaba da samun damar shiga kafafen sada zumunta ta hanyar amfani da VPN, wata manhaja da ke taimaka wa masu amfani da intanet wajen ɓoye ko sauya hanyar haɗuwarsu da intanet. Kamfanin Proton, mai samar da irin wannan sabis, ya bayyana cewa an samu ƙarin kashi 60,000 cikin ɗari na saukar da manhajar VPN ɗinsa a ranar da ta biyo bayan fara aiwatar da dokar hana amfani da kafafen sada zumunta.

HAC ta ce an ayyana dakartawar ne domin “ba wa gwamnati damar daidaita tsarin dokokinta, ta yadda za ta fi samun damar tsara yadda ake amfani da kafafen sada zumunta.”

Yanzu haka, gwamnati ta buƙaci masu amfani da kafafen sada zumunta su gabatar da takardun shaidarsu, matakin da a aikace ya kawo ƙarshen amfani da waɗannan kafafe ba tare da bayyana ainihin wane ne mutum ba.

HAC ta ce tana aiki tare da kamfanin Meta, wanda ya mallaki Facebook da Instagram, da kuma TikTok da YouTube, domin “inganta sa ido da tace abubuwan da ake wallafawa” a waɗannan kafafe.

’Yan adawar gwamnatin Gabon sun yi kakkausar suka kan matakin hana amfani da kafafen sada zumunta da gwamnatin Shugaba Brice Oligui Nguema ta ɗauka, suna mai bayyana shi a matsayin amfani da iko ta hanyar da ba ta dace ba.

Sai dai hukumomin ƙasar sun yi watsi da zarge-zargen, inda suka ce matakin ya zama dole domin samar da zaman lafiya da tabbatar da bin doka da oda a cikin al’umma.

#