An bude taron tuntubar junan karo na shida don samar da zaman lafiya a Sudan a ranar Laraba, inda kasashe da kungiyoyin kasa da kasa suke ganawa.
An bude taron tuntubar junan karo na shida don samar da zaman lafiya a Sudan a ranar Laraba, inda kasashe da kungiyoyin kasa da kasa suka taru don karfafa kokarin diflomasiyya, kawo karshen hare-hare da goyon bayan tsarin da zai tafi da kowa don kawo karshen rikicin.
Yayin da yake jawabi a wajen taron, Sakataren Harkokin Wajen Switzerland, Alexandre Fasel, ya bayyana cewa yakin da ke gudana a Sudan ya shiga shekararsa ta hudu, yayin da yanayi mai kama da yunwa ke ci gaba da wanzuwa a yankunan Darfur, Kordofan, da sauran sassan kasar.
Fasel ya yi gargadin cewa rikicin na kara barazana ga kwanciyar hankalin yankin, tare da haifar da tasirin da ya ketare iyakokin kasa zuwa kasashen da ke makwabtaka da Sudan.
"Yakin ba mutanen Sudan kadai kadai yake shafa ba; barazana ce ga kwanciyar hankalin yankin baki daya," in ji shi.
An tsugunar da miliyoyin mutane
Da yake bayyana lamarin a matsayin daya daga cikin munanan matsalolin jinkai da kariya da suka fi kamari a duniya, Fasel ya ce sama da mutane miliyan 15 ne suka rasa matsugunansu a cikin Sudan da kuma iyakokinta.
Ya jaddada cewa fararen hula na ci gaba da illatuwa daga rikicin, yana mai jaddada cewa kariya da damar da suke da ita ga jinkai ba dole ba ne ta kasance bisa sharadin tsagaita wuta ko sulhu n siyasa.
Fasel ya ce akwai yarjejeniya mai karfi cewa ba za a iya warware rikicin ta hanyar soji ba, yana mai jaddada bukatar tattaunawa wadda "ke karkashin jagorancin Sudan kuma ta kunshi kowa da kowa."
Pekka Haavisto, wakilin Sakatare Janar na MDD kan Sudan, ya ce taron ya samar da dama don tantance kokarin hadin gwiwa, magance kalubalen da ake fuskanta da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin shirye-shiryen diflomasiyya.
Karin yunkurin samar da zaman lafiya
Ya jaddada cewa ya kamata ƙoƙarin ƙasashen duniya ya taimaka wa juna tare da ba da gudunmawa ga manufar da aka cim ma ta kawo ƙarshen yaƙin, rage wa al'ummar Sudan radadin wahalar da suke sha da kuma tabbatar da makoma bisa ga zaman lafiya, tsaro, da mutunci a cikin haɗin kan Sudan.
Haavisto ya ce tattaunawar kan rage radadin za ta mayar da hankali kan gano matakan da suka dace da kuma ƙarfafar juna don gina kwarin gwiwa da kuma samar da yanayi mai kyau ga tsagaita wuta gaba ɗaya.
Da yake mayar da hankali kan ɓangaren yankin na rikicin, Haavisto ya ce dangantakar da ke tsakanin Sudan da ƙasashen da ke makwabtaka da ita ta sa tasirin yaƙin ya tsallake iyakokinta.
Sudan ta tsunduma cikin yaƙi tsakanin sojoji da rundunar sojojin sa kai ta Rapid Support Forces (RSF) tun daga watan Afrilun 2023, yakin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane. An danganta cin zarafin haƙƙin ɗan adam da kuma mace-mace mai yawa ga RSF.

