Daraktan Sadarwa na Turkiyya, Burhanettin Duran, ya ce Isra'ila na amfani da labaran ƙarya da kuma sauya bayanai a kafafen sadarwa na zamani domin ɓoye ɓarnarta a Gaza, yayin da kuma take kai hare-hare da makirci kan Shugaba Recep Tayyip Erdogan.
Daraktan Sadarwa na Turkiyya, Burhanettin Duran ya bayyana cewa Isra'ila na gudanar da tsare-tsaren yaɗa labaran ƙarya domin ɓoye kisan kiyashin da take aikatawa a Gaza.
Ya ƙara da cewa hare-haren da jami'an Isra'ila ke kaiwa kan Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, na nuna gazawar gwamnatin ƙasar.
Da yake jawabi a wani taron ƙasa da ƙasa mai taken "Fuska Biyu ta Isra'ila: Kisan Kiyashi da Yaɗa Labaran Ƙarya", wanda aka gudanar a Ankara, Duran ya yi magana kan cikar shekaru 38 da ayyana ƙasar Falasɗinu.
Ya jaddada goyon bayan Ankara ga kafa ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta bisa yarjejeniyar iyakoki ta shekarar 1967, wadda Gabashin Kudus da Isra'ila ta mamaye zai zama babban birninta.
Duran ya ce ayyukan Isra'ila tun daga shekarar 1948 sun kasance babban bala'i, yana mai cewa ɓarnar da take yi ba ta tsaya ga al'ummar Musulmi kaɗai ba, har ma ta shafi wuraren ibada, da harsuna da kuma tsoffin al'adu.
Yawan waɗanda aka kashe da karya yarjejeniyar tsagaita wuta
Duran ya ce, "Adadin fararen-hula da hare-haren Isra'ila suka kashe ya haura 74,000."
Ya bayyana cewa sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa fiye da 1,600 tare da jikkata wasu 5,000 tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 10 ga Oktoba, 2025.
Ya ce harin sama na baya-bayan nan da aka kai asibitin Nasser ya kasance babban keta yarjejeniyar tsagaita wutar.
Ya kuma bayyana cewa an kashe 'yan jarida fiye da 260 da ma'aikatan kiwon lafiya 1,700 a Gaza, yayin da iyalai ke fuskantar matsanancin yanayin sanyi a lokacin hunturu a sansanonin da ambaliyar ruwa ta mamaye.
Duran ya kalubalanci masu sa ido daga ƙasashen waje da su shafe sa'o'i 48 a Ramallah ko Hebron domin ganin yadda ake tsayar da ababen hawa a shingayen binciken sojoji da kuma sansanonin tsare mutane.
"A takaice, za su ga wani katon gidan yari ne da aka killace a bainar jama’a," in ji shi.
Da yake magana kan kalaman wasu jami'an Isra'ila da suka soki Shugaba Erdogan bayan jawabinsa a taron COP31 da kuma babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya, Duran ya ce:
Yana mai kari da cewa "Maimakon mayar da hankali kan gaskiya, harin da gwamnatin Isra'ila ke yi kan shugabanmu alama ce karara ta raunin da ta fada ciki."
Jami'an taron sun bayyana yadda Isra'ila ke amfani da gaggamin neman rinjayar tunanin jama'a, da fasahar AI da kuma dabarun sarrafa tsarin yada bayanai a kafafen sadarwa domin karkatar da gaskiya.
Duran ya ce Cibiyar Yaƙi da Yaɗa Labaran Ƙarya ta Hukumar Sadarwa ta Turkiyya ta karyata sama da labaran ƙarya 250 da ake dangantawa da Isra'ila, ciki har da rahotannin da aka janye na cewa an fille kan jarirai da kuma zargin cewa akwai cibiyar dakarun soji a cikin asibitoci.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: AA

