Mazauna yankin sun ce maharan sun kutsa cikin unguwar ne a daidai lokacin da Musulmi ke gudanar da sallar asuba, inda suka riƙa harbe-harbe ba kakkautawa, lamarin da ya tilasta wa jama'a tserewa domin tsira da rayukansu.
Wasu ’yanbindiga sun kashe wani babban hadimin Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, a wani hari da suka kai wata unguwar a arewa maso yammacin Najeriya.
An bayyana mamacin da sunan Hon. Nasiru Sani Kaura, wanda ke riƙe da muƙamin Babban Mataimaki na Musamman ga gwamnan. An ruwaito cewa an harbe shi har lahira ne lokacin da wasu mahara ɗauke da makamai suka kai hari yankin Low Cost da ke garin Kaura Namoda da sanyin safiyar Lahadi.
Mazauna yankin sun ce maharan sun kutsa cikin unguwar ne a daidai lokacin da Musulmi ke gudanar da sallar asuba, inda suka riƙa harbe-harbe ba kakkautawa, lamarin da ya tilasta wa jama'a tserewa domin tsira da rayukansu.
An ce Kaura, wanda ɗan siyasa ne da ke da tasiri a matakin al'umma kuma jagoran al'umma, ya rasa ransa a yayin harin. Rasuwarsa ta jefa al'ummar yankin cikin alhini, inda daga bisani aka gudanar da jana'izarsa bisa tsarin addinin Musulunci.
Kisan ya sake haifar da damuwa kan tabarbarewar tsaro a Kaura Namoda da sauran sassan Arewacin Zamfara, inda al'ummomi ke ci gaba da fuskantar hare-haren 'yanbindiga, kashe-kashe da sace mutane.
Mazauna yankin sun yi kira ga gwamnatin jihar da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'a, musamman a unguwannin da ake zaune.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: Others

