A cikin jawabin da ya gabatar a zaman, Garcia ya bayyana zaɓen a matsayin ɗaya daga cikin ƙalubalen da ka iya kawo cikas ga ƙoƙarin magance matsalolin tsaro a Nijeriya. Ya yi gargaɗin cewa ƙaruwar rikicin siyasa na iya haddasa tashin hankali.
Amurka ta bayyana damuwarta kan yiwuwar barkewar rikici yayin zaɓen shugaban ƙasar Nijeriya da za a gudanar a watan Janairu, inda ta tabbatar wa ‘yan majalisa cewa za ta sanya ido sosai kan yadda za a gudanar da zaɓen.
Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da Afirka, Frank Garcia, ne ya bayyana wannan damuwa yayin zaman sauraron bahasi da wani ƙaramin kwamitin Majalisar Wakilan Amurka mai kula da harkokin Afirka ya gudanar a ranar Alhamis, kan matsalar rikici da tashin hankali a Nijeriya.
A cikin jawabin da ya gabatar a zaman, Garcia ya bayyana zaɓen a matsayin ɗaya daga cikin ƙalubalen da ka iya kawo cikas ga ƙoƙarin magance matsalolin tsaro a Nijeriya. Ya yi gargaɗin cewa ƙaruwar rikicin siyasa na iya haddasa tashin hankali.
Ya ce: “Ina kallon ƙalubalen da ke gabanmu bisa hakikanin yadda suke. Misali, Nijeriya za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a watan Janairu, wanda ka iya haddasa tashin hankali.”
Ya kuma bayyana matsin lamba da ke kan tsarin tsaron Nijeriya, ƙarancin jami’an shari’a a wasu sassan yankin Tsakiyar Nijeriya da kuma ƙarancin kuɗaɗen gudanar da ayyuka a matsayin manyan matsalolin da ke kawo cikas ga yaƙi da matsalar rashin tsaro da ta daɗe tana addabar ƙasar.
Jawabin Garcia na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen duniya ke ƙara nuna damuwa kan hare-haren da ake kai wa al'ummomin Kiristoci da kuma matakan da Nijeriya ke ɗauka bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya ƙasar cikin jerin ƙasashen da ake zargin ana tauye 'yancin addini a cikinsu a ranar 31 ga Oktoban 2025.
A yayin zaman sauraron bahasin, ɗan majalisar wakilan Amurka, Riley Moore, ya buƙaci Washington ta mayar da hankali musamman kan abubuwan da za su gudana yayin zaɓen shugaban ƙasar mai zuwa, yana mai jaddada muhimmancin sanya ido sosai kan tsarin zaɓen.
Moore ya ce: “Ya kamata mu sanya ido sosai kan wannan zaɓen shugaban ƙasar, kamar yadda shaho ke sa ido kan abin da yake farautarsa. Ni zan sanya ido a kansu, kuma ya kamata dukkanmu mu sanya ido.”
Da yake mayar da martani, Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da dimokuraɗiyya, 'yancin ɗan Adam da ƙwadago, Riley Barnes, ya ce tuni ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta fara shirye-shiryen sanya ido ta hanyar wani keɓaɓɓen kwamiti da ke bibiyar zaɓuka a sassa daban-daban na duniya.
Ya bayyana zaɓen Nijeriya a matsayin wadda ke da matuƙar muhimmanci ga Amurka, inda ya tabbatar wa 'yan majalisar cewa ma'aikatar za ta sanya ido sosai kan dukkan abubuwan da za su faru yayin gudanar da zaɓen.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: Others

