Shugaban ya kuma sha alwashin cewa Ankara za ta ci gaba da ƙoƙarin da take yi na samar da zaman lafiya a Libya inda ya jaddada cewa babu wata manufa wadda jama’ar Libya ke adawa da ita da za ta yi nasara.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da Firaministan Libya Abdulhamid Dbeibah a ranar Alhamis sun tattauna kan batutuwan da suka shafi yanki a gefen taron COP31 da ake gudanarwa a birnin Antalya na Turkiyya.
Erdogan ya bayyana cewa Turkiyya da Libya za su ci gaba da ɗaukar matakai domin yauƙaƙa dangantaka a tsakaninsu da kuma ci gaba da neman hanyoyin samar da manufofi waɗanda za su ƙara ƙarfin alaƙa musamman a fannin makamashi.
Shugaban ya kuma sha alwashin cewa Ankara za ta ci gaba da ƙoƙarin da take yi na samar da zaman lafiya a Libya inda ya jaddada cewa babu wata manufa wadda jama’ar Libya ke adawa da ita da za ta yi nasara.
Ya kuma jaddada cewa Turkiyya ba za ta amince da duk wani tsari da ya ci karo da muradun Libya ba.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan, Ministan Tsaron Turkiyya Yasar Guler, Shugaban Leƙen Asirin Turkiyya Ibrahim Kalin da kuma Daraktan Sadarwa na Turkiyya Burhanettin Duran duk sun halarci wannan tattaunawa.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: Anadolu Agency (Wire)
