n samar da sabbin takardun kuɗin ne da takarda ta musamman mai ƙarfi, domin su jure yawan amfani da kuma yanayin zafi da damshin ƙasar, lamarin da ake sa ran zai rage lalacewarsu da kuma kuɗin sake buga sababbi.
Ghana ta ƙaddamar da sabbin takardun kuɗi masu ƙaramin girma da kuma ɗorewa, tare da inganta matakan kariya daga jabun kuɗi da kuma ƙawata su da alamomin tarihi da al'adun ƙasar.
Babban Bankin Ghana ya ce sake fasalin takardun kuɗin ya zama dole saboda wasu daga cikin tsoffin ƙirar kuɗin sun shafe sama da shekaru 20 suna yawo a hannun jama'a, a daidai lokacin da fasahar yin jabun kuɗi da ƙa'idojin tsaro na ƙasashen duniya ke ci gaba da bunƙasa.
An samar da sabbin takardun kuɗin ne da takarda ta musamman mai ƙarfi, domin su jure yawan amfani da kuma yanayin zafi da damshin ƙasar, lamarin da ake sa ran zai rage lalacewarsu da kuma kuɗin sake buga sababbi.
Haka kuma, an inganta alamomin da ake iya taɓawa a jikin takardun domin taimaka wa masu matsalar gani wajen bambance nau'ikan kuɗin.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da sabbin takardun, Shugaban ƙasar John Mahama ya ce ƙananan girmansu zai sauƙaƙa amfani da su a harkokin kasuwanci da sauran mu'amalolin yau da kullum.
Gwamnan Babban Bankin Ghana, Johnson Asiama, ya ce za a fara amfani da sabbin takardun, waɗanda ake kira 'Heritage Series', daga ranar 1 ga Disamba, tare da tsoffin takardun kuɗin da za su ci gaba da kasancewa halastattun kuɗaɗe.
Sake fasalin ya shafi dukkan nau'ikan takardun kuɗi guda takwas, daga cedi ɗaya zuwa cedi 200, ciki har da dawo da takardar cedi biyu.
Sai dai bankin ya jaddada cewa wannan sauyi ba ya nufin an sauya darajar kuɗin ƙasar ko kuma an rage adadin kuɗin da ake da su a kasuwa.
Baya ga inganta tsaro, sabbin takardun kuɗin za su ƙunshi hotunan fitattun 'yan ƙasar da suka taka rawa a tarihi, ciki har da tsohon sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Kofi Annan, da shugaban ƙasar na farko, Kwame Nkrumah, tare da wasu muhimman wuraren tarihi da abubuwan tunawa.
Ghana ta fara amfani da cedi a matsayin kuɗin ƙasarta a watan Yulin 1965, shekaru takwas bayan samun 'yancin kai daga Birtaniya.
Ƙaddamar da sabbin takardun kuɗin na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke ƙara faɗaɗa amfani da hanyoyin biyan kuɗi ta intanet da na zamani.
Duk da haka, Gwamnan Babban Bankin ya jaddada cewa kuɗin hannu na ci gaba da kasancewa muhimmin ɓangare na tsarin tattalin arzikin ƙasar.
Ya yi gargaɗin cewa hare-haren kutse ta intanet, matsalolin fasaha da bala'o'in yanayi na iya kawo cikas ga hanyoyin biyan kuɗi na zamani.
A wani mataki na ƙarfafa kariya ga kuɗin ƙasar, Babban Bankin Ghana na kuma shirin samar da sabuwar doka da za ta maye gurbin dokar kuɗi ta shekarar 1964, domin ƙara tsaurara matakan hukunta masu yin jabun kuɗi da waɗanda ke lalata ko amfani da takardun kuɗi ba bisa ƙa'ida ba.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: Ghana News Agency

