Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taron tattaunawa da aka gudanar a cibiyar Chatham House da ke birnin Landan, tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Kimpact Development Initiative.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta sanya ranar 28 ga Nuwamban 2026, domin gudanar da gwajin tantance masu zaɓe da kuma kaɗa ƙuri’a a fadin kasar, a wani mataki na tantance ingancin sabbin gyare-gyaren da ta yi wa na’urar tantance masu kaɗa kuri’a ta BVAS da kuma tsarin aika sakamakon zaɓe ta intanet.
Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taron tattaunawa da aka gudanar a cibiyar Chatham House da ke birnin Landan, tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Kimpact Development Initiative.
Taken taron shi ne, “Zaɓen Nijeriya na 2027: Tafarkin Dimokuraɗiyya da Zaman Lafiyar Yankin Bayan Kada Ƙuri’a.”
A cewar wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai kuma mai ba shugaban INEC shawara kan harkokin yaɗa labarai, Adedayo Oketola, ya fitar a Abuja, Amupitan ya ce gwajin zai mayar da hankali ne kan yadda zaɓen shugaban ƙasa zai gudana, domin bai wa hukumar damar tantance ingancin tsarin tantance masu kaɗa ƙuri’a da kuma aika sakamakon zaɓe ta intanet kafin babban zaɓen.
Shugaban INEC din ya kuma bayyana cewa hukumar ta bullo da wasu matakan kariya na fasaha domin hana loda sakamakon rumfunan zabe marasa inganci da kuma alkaluman da ke nuna an kada kuri’a fiye da adadin masu kada kuri’ar da aka yi wa rajista a rumfar.
Ya ce wani bincike da hukumar ta gudanar bayan zaben 2023 ya gano cewa cibiyoyin tattara sakamako, ba rumfunan zabe ba, su ne suka fi haddasa matsalolin gudanarwa da tattara sakamakon zabe.
A cewarsa, hukumar ta yanke shawarar inganta fasahar zaben da take amfani da ita a halin yanzu, maimakon bullo da wata sabuwar fasaha gaba daya, saboda karancin lokacin da ya rage kafin zaben 2027.
Dangane da korafe-korafen da aka samu kan tangardar da na’urar BVAS ta yi a lokacin babban zaben 2023, Amupitan ya ce INEC na gina wuraren ajiya masu tsarin sanyaya iska a jihohin kasar domin kare na’urorin daga matsanancin zafi.
Ya kara da cewa hukumar ta sayi karin na’urorin BVAS, tare da rage yawan masu kada kuri’ar da kowace na’ura za ta tantance daga mutum 1,250 zuwa 850.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: Others

