Joseph Blatter na neman a bincika ko Donald Trump yana taka babbar rawa wajen jan akalar Infantino, har yake cewa yana tunanin lamura sun fara ɓaci ne tun bayan faruwar kusancin shugaban FIFA da Trump.

Tsohon shugaban FIFA, Joseph Blatter, ya kira Infantino da "mahaukaci"

Tsohon shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, Joseph S. Blatter, ya yi mummunar suka kan shugaban FIFA na yanzu, Gianni Infantino, inda ya kira shi da ɗan kama-karya.

Blatter, wanda a yanzu yake da shekaru 90 a duniya, ya kamanta Infantino a matsayin sarkin girman-kai, wanda “ba ya barin kowa ya hau lif tare da shi. Kuma ba wanda ya isa ya soke shi".

Infantino shi ne ya gaji Blatter a shekarr 2026, amma a yau Blatter na zargin sa da “wanda bai san wani kaidi ba.” Blatter ya ce, "[Infantino] Bai san komai kan [dokokin ƙwallo] ba. Ina nufin, ya kamata a tura Infantino asibitin mahaukata."

Kalaman na Blatter sun mayar da hankali kan abin da ya kira take dokokin ƙwallo da yake zargin mutumin da ya gaje shi da aikatawa. Sannan ya yi nuni da yadda dokokin ƙwallo suke, maimakon sukar hankalin Infantino.

Da yake nuni da dacewar kai Infantino gaban Kotun Warware Jayayya kan Wasanni, CAS, wadda ke Lausanne, Blatter ya ce a zahiri halayyar shugaban FIFA na yanzu ta saɓa wa dokokin FIFA.

Magajin Infantino

"Bai tuntuɓi kowa ba gabanin ƙaddamar da Kyautar Zaman Lafiya. Wannan wani abu ne da ya wajaba a kawo shi gaban kotun CAS."

Batun ƙirƙirar kyautar zaman lafiya da FIFA ƙarƙashin Gianni Infantino ta ɓullo da shi a Disamban 2025, batu ne da ya samu suka daga ɓangarori da dama, musamman bayan an bai wa shugaban Amurka, Donald Trump kyautar.

Wannan ne ya sa Joseph Blatter ke bukatar a bincika ko Donald Trump yana taka babbar rawa wajen jan akalar Infantino, har yake tunani lamura sun fara ɓaci ne tun bayan kusancin shugaban FIFA da Trump.

A kalaman da ya yi kan Infantino, Blatter ya ce "Yana da imanin cewa an zaɓe shi ne don ya kankane harkar wasanni da ta fi farin jini a duniya. Amma akwai manyan jami’an hukumar ƙwallon ƙafa waɗanda ba su aminta da wannan ba. Suna son su cire shi."

Sai dai shi kansa, Sepp Blatter, an tilasta masa barin shugabancin FIFA ne 2015, kafin Infantino ya hau kujerar a 2016. Amma a yanzu yana fatan a kori wanda ya gaje shi.

Amma duk da hukumomin ƙwallo a Turai suna burin matsa-lamba kan tsohon kocin Arsenal, Arsene Wenger ya shiga takara, zaɓin Blatter shi ne Sebastian Coe, shugaban hukumar kula da wasannin motsa-jiki, wanda ya faɗi takarar shugabancin IOC a 2025.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: Reuters (Wire)

#