A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Lahadi, Tinubu ya ce rahoton ya nuna ci gaba a fannonin bunƙasar tattalin arziki, kuɗaɗen shiga na gwamnati da kuma ajiyar kuɗaɗen waje.

Rahoton Bankin Duniya ya nuna ci gaba a sauye-sauyen tattalin arzikin Nijeriya: Tinubu

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ke aiwatarwa sun fara haifar da sakamako mai kyau, bisa bayanan da ke cikin rahoton Bankin Duniya na Oktoban 2026 kan tattalin arzikin ƙasar.

A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Lahadi, Tinubu ya ce rahoton ya nuna ci gaba a fannonin bunƙasar tattalin arziki, kuɗaɗen shiga na gwamnati da kuma ajiyar kuɗaɗen waje.

Rahoton mai taken Beyond the Federal Purse: How Higher Revenues Reshaped State Priorities ya bayyana cewa tattalin arzikin Nijeriya ya bunƙasa da kashi 4.2 cikin 100 a rubu’in farko na shekarar 2026, idan aka kwatanta da kashi 3.9 cikin 100 a daidai wannan lokaci na shekarar 2025.

Bankin Duniya ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai bunƙasa da matsakaicin kashi 4.4 cikin 100 a kowace shekara tsakanin 2026 da 2028, a cewar rahoton.

Haka kuma, Tinubu ya ce rahoton ya nuna cewa hauhawar farashi ta ragu daga kashi 27.6 cikin 100 a watan Janairun 2025 zuwa kashi 15.2 cikin 100 a watan Disamban wannan shekarar.

Sai dai rikicin Gabas ta Tsakiya ya haddasa tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya, lamarin da ya kawo cikas ga ƙoƙarin rage hauhawar farashi.

Bankin Duniya na hasashen cewa hauhawar farashin kayayyaki za ta ragu zuwa kusan kashi 12 cikin 100 nan da shekarar 2028.

Rahoton ya kuma nuna cewa rarar kuɗin da Nijeriya ke samu a ma'amalolinta da sauran ƙasashen duniya (current account surplus) ta kai dala biliyan 12 a rubu’in farko na shekarar 2026, kwatankwacin kashi 7 cikin 100 na jimillar kuɗaɗen da tattalin arzikin ƙasar ya samar (GDP). Wannan ya nuna ƙarin dala biliyan 8.6 idan aka kwatanta da adadin shekarar da ta gabata.

Haka kuma, ajiyar kuɗaɗen waje ta Nijeriya ta ƙaru daga dala biliyan 45.5 a ƙarshen shekarar 2025 zuwa dala biliyan 53.8 a watan Agustan 2026.

Ƙarin kuɗaɗen shiga ga jihohi

A cewar Tinubu, rahoton Bankin Duniya ya danganta ƙarin kashi 69 cikin 100 na kuɗaɗen da ake rabawa tsakanin matakan gwamnati, bayan cire tasirin hauhawar farashi, tsakanin shekarun 2023 da 2025, da sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar.

Ya ce gwamnatocin jihohi ne suka fi amfana da ƙarin kuɗaɗen, inda kashe kuɗaɗensu kan ayyukan raya ƙasa ya ƙaru da kashi 151 cikin 100 a wannan lokaci.

Tinubu ya ƙara da cewa an fi karkatar da kuɗaɗen ne zuwa ayyukan gine-ginen hanyoyi da sufuri, noma, makamashi da gidaje.

Rahoton ya kuma nuna cewa jihohi 29 cikin 33 sun ƙara ware kuɗaɗe domin samar da ababen more rayuwa da ke tallafa wa bunƙasar tattalin arziki.

Tinubu ya ce kuɗaɗen shiga na cikin gida sun ƙaru a zahiri a jihohi 31 cikin 35, yayin da jihohi 21 suka rage yawan bashinsu idan aka kwatanta da GDP ɗinsu tsakanin shekarun 2021 da 2025.

Sanarwar ta kuma ce ana sa ran jimillar bashin gwamnati zai ragu daga kashi 40 cikin 100 na GDP a shekarar 2025 zuwa kashi 38.1 cikin 100 a shekarar 2026.

Sauye-sauye da tsadar rayuwa

Tinubu ya ce sakamakon da rahoton ya nuna ya tabbatar da muhimmancin matakan da gwamnatinsa ke ɗauka, ciki har da cire tallafin man fetur, haɗa kasuwannin canjin kuɗaɗen waje da kuma ƙarfafa tsarin kula da kuɗaɗen gwamnati.

Sai dai ya amince cewa akwai sauran aiki domin tabbatar da cewa ci gaban tattalin arzikin ya inganta rayuwar al'umma, musamman ta hanyar rage farashin abinci da samar da ayyukan yi ga matasa.

Shugaban ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da faɗaɗa shirin bayar da tallafin kuɗi kai tsaye ga gidaje masu buƙata, inganta ayyukan noma da kuma faɗaɗa damar samun kiwon lafiya mai araha da ingantaccen ilimi.

Rahoton Bankin Duniya ya fito ne a daidai lokacin da Nijeriya ke ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da nufin ƙara kuɗaɗen shiga na gwamnati, bunƙasa tattalin arziki da kuma magance matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa ke haifarwa.

#