A shekarun baya, Pochettino ya kasance cikin jerin koci-kocin da suka so karɓar ragamar Manchester United har karo uku, a 2016, 2019, da 2024.

Pochettino ya shirya zama kocin Manchester United, idan aka sallami Michael Carrick

Yayin da kocin Manchester United, Michael Carrick ke fuskantar babbar barazanar sallama daga ƙungiyar, rahotanni na cewa kocin tawagar Amurka, Mauricio Pochettino, ya shirya amsa tayin karɓar ƙungiyar idan an masa.

Duk da cewa ba daɗewa Pochettino ya sanya hannu kan kwantiragi mai tsawo har zuwa 2030 tare da Amurka, kocin ɗan asalin Argentina ya shirya komawa gasar Firimiya ta Ingila, cewar rahotanni.

Kocin Manchester United, Michael Carrick, yana jiran sanin makomarsa a ƙungiyar, bayan da ya gaza farfaɗo da tagomashinta, inda a ƙarƙashinsa take fuskantar mafi munin sakamako a farkon gasar Firimiya.

Hasali ma, wasa ɗaya kacal Carrick ya lashe cikin wasanni 10, wanda ya jefa United cikin rukunin ƙungiyoyi uku na ƙasan teburi, waɗanda za su faɗo daga gasar.

Sai dai duk da cewa Carrick ya ci gaba da nuna ko-in-kula kan barazanar sallamarsa, a ranar Talata majiyoyi sun nuna cewa a yanzu shuwagabannin United suna shirin sallamar sa.

Neman zama koci

Michael Carrick shekarunsa 45, kuma tsohon ɗanwasan tsakiya ne a United da kuma tawagar Ingila, amma zuwansa United a bazarar bana ba ta yi armashi ba.

Shi kuwa Pochettino ƙwararre ne kan gasar Firimiya, saboda ya jagoranci Tottenham da Chelsea na tsawon lokaci, kafin ya riƙe Paris Saint-Germain ta Faransa.

A shekarun baya, Pochettino ya kasance cikin jerin koci-kocin da suka so karɓar ragamar Manchester United har karo uku, a 2016, 2019, da 2024.

Kocin mai shekaru 54, zai yi amfani da saɗarar cikin kwantiraginsa da ta ba shi damar ajiye aiki a Amurka, kuma ya koma wata ƙungiyar kan farashin da ya kai dala miliyan $10.

A halin yanzu, Pochettino ya mayar da hankali kan jagorantar tawagar Amurka a wasan da za su buga tare da Haiti a gasar Concacaf ta ƙasasehn nahiyar Arewacin Amurka, ranar Asabar mai zuwa a Miami.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: TRT Afrika Français

#