Ministan ya kuma bayyana burin Ghana na kafa wata cibiyar tafiya domin jinya a shekarar 2027 domin jan hankalin masu jinya daga ƙetare da kuma faɗaɗa samar da kula da lafiya na musamman.

Ghana za ta kashe dala miliyan 200 kan shirya wa shirin makamashin nukiliya

Ghana ta shirya domin zuba jari na dalr Amurka miliyan $200 a wani shiri n awatanni 24 don shirya ƙasar don gina tashar makamashin nukiliyarta ta farko.

Shirinda za a fara daga watan Janairun 2027 zuwa watan Disambar 2028, ana tsammanin zai kai ga rattaɓa hannu kan yarjejeniyoyin aikin injiniya da na sayayya da na gini da kuma na samar da kuɗi don rashar makamashin nukiliya mallaƙr ƙasar.

Kamfanin dillancin labaran ya ba da rahoton cewa Ministan Kuɗin Ƙasar, Dr Cassiel Ato Forson, ne ya bayyana wannan yayin da yake gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2027 da manufar tattalin arzikin ƙasar ga Majalisar Dokokin ranar Alhamis.

Ya ce aikin zai haɗa da tabbatar da dacewar wuri da zaɓr fasaha da tatancewa muhalli da samar da kudi da ba da lasisi da matakan tsaro da shirin ko ta kwana da buƙatu na tsaro.

"Nan zuwa watan Disamban shekarar 2028, burinmu shi ne mu cikakken shiri wa makamashin nukiliya da kum arattaɓa hannu kan yarjejeniyoyi na injiniya da sayayya da gini da samar da kuɗi don tashar makamashin nukiliya mallaƙr ƙasa," kamar yadda kamfanin dillancin labaran ya ambato shi yana cewa.

Dr Forson ya bayyana cewa kammla shiryawa ba ya nufin cewa za a fara samun lantarki a shekarar 2028, amma zai sa ƙasar ta shirya don shiga yarjejeniyar gini.

Ya ce tashar za ta kasance muhimmiyar ƙadara ta ƙasa kuma za ta yi aiki ne a ƙarƙashin tsarin Mai Samar Da Makmashi Mai Zaman kanta (IPP).

Abokan hulɗa na ƙtare za su ba da fasaha da kuɗi da aikin ƙwararru yayin da gwamnati za ta kasance mai mallakar aikin, kamar yadda ya bayyana .

Kazalika gwamnatin na shirin horas da fiye da masana kimiyya ‘yan Ghana fiye da 2,000 domin samar da ƙarewa na cikin gida wa shirin na nukiliya.

"‘Yancin kai na makamashi na nufin dole ne Ghana ta kasance tana da iko kan samarwa da tura lantarkin da ke tuƙ tattalin arzikinmu," in ji shi.

Ghana tana sa ran shigar da tashar nukiliyarta ta farko cikin tsarin wutar lantarkinta nan da shekarar 2030.

An bayyana Nsuban a lardin Yammacin Ƙasar a matsayin wurin da aka fi so a yi aikin, inda kuma aka zaɓi Obotan a Lardin Tsakiyar Ƙasar a wani wuri da za a iya amfani da shi a madadin inda aka fi so, bayan binciken da masana ‘yan Ghana suka yi.

Shiroin na biyo bayan shekar da Shuga John Dramani Mahama ya yi ne a watan Oktoban shekarar 2026 cewa Ghana ta fara tattaunawa da Kamfanin Mkamashin Nukiliya na Ƙasa na Rasha, Rosatom, kan gina tashar makamashin nukiliya ta ƙasar ta farko.

Ghana na son a rinƙa zuwa jinya ƙasar daga ƙetare

Ministan ya kuma bayyana burin Ghana na kafa wata cibiyar tafiya domin jinya a shekarar 2027 domin jan hankalin masu jinya daga ƙetare da kuma faɗaɗa samar da kula da lafiya na musamman.

Shirin ana son yin sa ne domin sa ƙasar ta kasance wani wurin zuwa jinya ta hnayar kawo kayayyakin asibiti da na masauƙin baƙi.

Dr Cassiel Ato Forson ya cecibiyar da aka shirin yi zai haɗa asibitocin ƙararru da wuraren bincike da wuraren gyara jiki da otel-otel da ɗakunan gwaje-gwaje da wuraren ba da magunguna domin ba da damar wata hidima da ta haɗa komai da komai.

Gwamnatin kuma za ta ba da ƙarin gwiwa na haraji da fili da ake kula da shi da muhimman ababen more rayuwa domin tallafa wa gina cibiyar.

Dr Forson ya ce ana sa ran cewa shirin zai ƙara yawan masu shigowa ƙsar daga ƙetare da ƙarfafa daɗewar baƙi da kuma haɓka yawon buɗe ido nan da shekarar 2030.

Ya ce fa’idodin yawon buɗe ido don jinya ya kamata ya zarce samar da kayayyakin jinya zuwa sauran fannonin tattalin arziki.

Ana tsammanin manoma na cikin ƙasar da masu smaar da abinci da masu aikin sufuri da zane da masu aikin hannu da ma ‘yan kasuwa za su amfana daga damarmakin da tsarin zai samar.

Aikin wani ɓangare ne na tsare-tsaren gwamnatin na faɗaɗa tattalin arziki da kuma ƙarfafa fannin hidima na ƙasar.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: Ghana News Agency

#