Faɗa tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga da ’yan sa-kai ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 50 a Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Nijeriya, kamar yadda wasu mazauna yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Asabar. Majiyoyin

Faɗa tsakanin 'yanbindiga da 'yan sa-kai ya yi ajalin mutum fiye da 50 Jihar Zamfar ta Nijeriya

Faɗa tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga da ’yan sa-kai ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 50 a Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Nijeriya, kamar yadda wasu mazauna yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Asabar.

Majiyoyin sun ce ’yan sa-kai daga ƙauyen Zoma da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum sun yi wa ’yanbindigar kwanton ɓauna ne, yayin da suke wucewa ta ƙauyen a ranar Alhamis, bayan sun yi garkuwa da wasu mutane a ƙaramar hukumar Gummi mai maƙwabtaka.

“An sanar da mu cewa ’yanbindigar na kan hanyarsu ta zuwa yankinmu, lamarin da ya sa ’yan sa-kan suka yi musu kwanton ɓauna, inda aka fafata da musayar wuta mai tsanani,” a cewar wani mai rike da sarautar gargajiya na yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro.

Ya ce, “’Yan sa-kanmu sun kashe ’yanbindiga 44, yayin da mu ma muka rasa ’yan sa-kai tara a wannan faɗan,” a cewar masaraucin, inda ya ƙara da cewa an kuma kashe wani fitaccen kwamandan ’yanbindiga mai suna Jijji a fafatawar, wanda ya jagoranci sace mutanen.

Yaƙi da ’yan bindiga

Wasu mazauna ƙauyen Zoma, waɗanda AFP ta zanta da su, sun tabbatar da irin wannan bayani game da arangamar da kuma adadin waɗanda suka mutu.

Sojojin Nijeriya na kira ’yanbindiga da “’yan ta’adda”, kuma suna gudanar da wani aiki na musamman na yaƙi da su a yankin arewa maso yammacin ƙasar.

Taɓarɓarewar tsaro da tsadar rayuwa sun zama manyan batutuwan da ke jan hankali a yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da ake gudanarwa, yayin da Bola Tinubu ke neman zarcewa a wa’adi na biyu a zaɓen watan Janairu.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: Wasu ‘yan bijilanti da ke aiki a kan hanyar Jihar Neja waɗanda ke taimakawa samar da tsaro

#