Shirin ya kunshi tsarin da zai jagoranci manufofin tsaro na dogon lokaci, tare da daidaita bukatun soji, ayyukan tsaro da kashe kudade bisa la’akari da kalubalen tsaron da Nijeriya ke fuskanta a yanzu da kuma gaba.

Majalisar yaƙin neman zaɓen APC ta ƙaddamar da shirin samar da tsaro na Tinubu na shekaru biyar

Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC a Nijeriya ya sanar da wani sabon shirin tsaro na shekara biyar ƙarƙashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu da nufin magance matsalar rashin tsaro da ta dade tana addabar ƙasar, ta hanyar faɗaɗa ƙarfin sojoji, da inganta tattara bayanan sirri da kuma daidaita ayyukan hukumomin tsaro.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Dele Alake, mai magana da yawun ƙwamitin yakin neman zaben shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, ya fitar a ranar Lahadi kan matakan da gwamnatin ke dauka wajen magance matsalar tsaro.

‘‘Shugaba Bola Tinubu ya ƙuduri aniyar kawo karshen matsalar rashin tsaro da aka kwashe shekaru 17 tana addabar sassan Nijeriya, ta hanyar aiwatar da cikakken tsarin dabarun tsaro na shekaru biyar,’’ in ji sanarwar.

Majalisar ta ce, ‘‘an tsara wannan shiri ne domin ƙarfafa tsarin tsaron ƙasar, tare da inganta ayyukan sojoji, da kuma tabbatar da daukar matakan da suka dace ta hanyar haɗin gwiwa wajen tunkarar barazanar da ka iya tasowa.’’

Haka kuma, sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da gwamnati ke ikirarin cewa, ayyukan soji a cikin shekaru uku da suka gabata sun kawar da ‘yanta’adda fiye da 15,000, ciki har da mambobin ƙungiyar Boko Haram.

Kazalika, gwamnatin ta ce fiye da mayakan Boko Haram da iyalansu 130,000 ne suka mika wuya ƙarƙashin shirin Operation Safe Corridor, wanda aka kafa domin gyara halayen tsoffin masu tada ƙayar baya da kuma taimaka musu su koma cikin al’umma.

A cewar kwamitin, gwamnatin na amfani da dabaru guda biyu, wato ci gaba da kai hare-haren soji kan ƙungiyoyin masu dauke da makamai da kuma aiwatar da shirye-shiryen da ba na yaki ba domin magance matsalar rashin tsaro.

Fadada karfin soji da yawan jami’ai

A wani bangare na kokarin karfafa rundunar sojin Nijeriya, Tinubu ya amince da kafa karin rundunonin soji guda hudu, lamarin da ya kara yawan rundunonin sojin kasar daga takwas zuwa 12.

Sabbin rundunonin, wadanda za su kasance a Makurdi, Ilorin, Jalingo da Benin City, na da nufin rage cunkoson gudanar da ayyukan soji a wasu wurare, tare inganta tsarin jagoranci da sa ido, da karfafa tsaron iyakoki da kuma bai wa sojoji damar mayar da martani cikin gaggawa kan barazanar tsaro.

Shugaban ya kuma amince da daukar karin sojoji 28,000 domin kara yawan jami’an da ke aikin tabbatar da tsaro da kuma inganta ƙarfin rundunar wajen gudanar da ayyukanta.

Domin tallafa wa wannan shirin daukar sabbin sojoji, an amince da kafa karin cibiyoyin horas da sojoji guda biyu a birnin Osogbo na jihar Osun, da Amasiri-Edda na jihar Ebonyi.Kowace daga cikin cibiyar za ta iya horas da sabbin sojoji 6,000 a lokaci guda, wanda hakan zai kai adadin wadanda za a iya horaswa a cibiyoyin biyu zuwa 12,000.

Kwamitin yakin neman zaben APC ya ce tuni sabbin dakaru 5,210 suka fara samun horo a cibiyar da ke Osogbo.

Haka kuma, Tinubu ya amince da daukar karin jami’an ’yan sanda 50,000 domin karfafa ayyukan rundunar da kuma inganta matakan dakile laifuffuka a sassan kasar.

Baya ga karin jami’an tsaro, gwamnatin na zuba jari a wajen gine-ginen gidajen sojoji da inganta walwalar jami’ai.

Daya daga cikin ayyukan shi ne gina barikin sojoji mai gidaje 700 a Ikere-Ekiti na jihar Ekiti, domin samar wa jami’an soji ingantattun wuraren zama da kuma muhimman kayayyakin more rayuwa da za su taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu.

Inganta bayanan sirri da hadin gwiwar hukumomin tsaro

A ƙarƙashin sabon shirin tsaro na shekaru biyar, ana sa ran gwamnatin tarayya za ta kara mayar da hankali kan tattara bayanan sirri, da sa ido, da amfani da fasahar zamani da kuma inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro.

Shirin na da nufin tabbatar da cewa ana amfani da kudaden da ake warewa bangaren tsaro bisa la’akari da barazanar da ake fuskanta da kuma bukatun ayyukan soji.

Haka kuma, ana sa ran zai taimaka wajen inganta shirin ko-ta-kwana na sojoji, tare da cike gibin kayan aiki da kuma rage almubazzaranci da kudaden gwamnati.

Wannan mataki ya biyo bayan umarnin da Tinubu ya bayar a watan Agustan 2026 na shirya cikakken nazari kan barazanar tsaron Nijeriya da kuma tsara ayyukan tsaro na shekaru biyar.

Shugaban ya kafa kwamitin mutum 11 karkashin jagorancin mai ba shi shawara kan harkokin tsaron cikin gida, Manjo Janar Adeyinka Famadewa, domin gano manyan barazanar tsaro, da tantance karfin sojoji da kuma bayar da shawarwari kan abubuwan da ya kamata a mayar da hankali a kai.

An bukaci kwamitin ya gabatar da rahotonsa da shawarwarin da ya tsara cikin kwanaki 90. Ana kuma sa ran tsarin zai zama jagora wajen tsara kasafin kudin tsaro da sayen kayan aikin soji a tsawon shekaru masu zuwa.

Matsalar rashin tsaro na ci gaba da zama babban kalubale

Duk da ikirarin gwamnatin na samun nasarori a ayyukan soji da karin zuba jari a bangaren tsaro, Nijeriya na ci gaba da fuskantar hare-haren ’yan tada kayar baya, da ’yanbindiga da sauran kungiyoyin masu aikata laifuffuka a sassa daban-daban na ƙasar.

Wasu alkaluman tsaro na baya-bayan nan sun nuna girman ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta ce an samu hare-hare wanda yakai ga salwanta rayuka 418 da sace mutane 227 cikin tsawon makonni takwas a watan Satumba da Oktoban 2026.

Tasirin rikicin ya kuma ketare iyakokin ƙasar, inda hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta bayyana cewa kusan mutane 64,000 ne suka tsere daga gidajensu a arewacin Nijeriya zuwa makwabciyarta Nijar tun farkon shekarar 2026 sakamakon tashe-tashen hankula.

Ci gaba da aukuwar wadannan hare-hare na kara janyo damuwa kan kariyar fararen hula, da matsalar gudun hijira da kuma ƙarfin hukumomin tsaro na dawo da zaman lafiya mai dorewa a yankunan da abin ya shafa.

A bangare guda kuma, sabon shirin tsaron na nuna wani gaggarumin yunkuri na gwamnatin Nijeriya na ƙarfafa matakan yaki da rashin tsaro.

Sai dai nasarar shirin za ta dogara ne da yadda za a aiwatar da shi, da samar da isassun kuɗaɗen aiwatarwa, da musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro da kuma yadda za a tabbatar da cewa ayyukan soji sun haifar da kariya mai dorewa ga fararen hula.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: TRT Afrika Hausa

#