Fadar Pretoria ta yi sammacin jakadan Nijeriya a ƙasar, Femi Fani-Kayode, bayan taƙaddamar da ta samo asali daga abin da ya faru a bikin miƙa takardar kama aiki da shugaba Cyril Ramaphosa ya karɓi baƙunci.
Ministan Harkokin Ƙasashen Waje da Haɗin-Gwiwa na Afirka ta Kudu, Ronald Lamola ya ce yana ɗaukar batun tsawatarwar diflomasiyya da aka yi wa jakadan Nijeriya, Femi Fani-Kayode, a matsayin abu da aka gama batunsa.
Amma ya ce Afirka ta Kudu za ta ci gaba da sa-ido kan lamarin, a cewar rahotannin gidan talabijin na ƙasar, SABC.
Fadar Pretoria ta yi sammacin Jakadan Nijeriya a ƙasar, Femi Fani-Kayode, bayan taƙaddamar da ta samo asali daga abin da ya faru a bikin da shugaba Cyril Ramaphosa ya karɓi baƙunci, don sabbin jakadu su miƙa takardar kama aiki.
A ranar 17 ga Nuwamban 2026, Fani-Kayode ya gana da Babban Daraktan Harkokin Ƙasashen Waje da Haɗin-gwiwa na Afirka ta Kudu, Zane Dangor, wanda ya isar da damuwar gwamnati kan wallafe-wallafe a soshiyal midiya da jakadan ya yi game da bikin a fadar gwamnati.
Yayin ganawa, Dangor ya tunatar da jakadan game da Yarjejeniyar Vienna kan mu’amalolin diflomasiyya, wadda ke buƙatar jakadu su kula da lamuran diflomasiyya a hukumance ta sanannun hanyoyin diflomasiyya.
‘Ganawar faram-faram’
Daga bisani, Fani-Kayode ya bayyana ganawar a matsayin “mai faram-faram kuma mai cike da alfanu”, inda ya ce ƙasashen biyu suna ci gaba da nuna aniyar ƙarfafa daɗaɗɗiyar alaƙarsu.
Amma me ne takamammen abin da ya haddasa taƙaddama tsakanin ƙasashen biyu na Afirka mafiya ƙarfin fada-a-ji?
Taƙaddamar ta fara ne ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba, lokacin da Ramaphosa ya karɓi takardun sabbin jakadu 15 da aka aika Pretoria.
Fani-Kayode, cikakken jakadan Nijeriya na farko da aka aika Afirka ta Kudu cikin kusan shekaru huɗu, ya zargi Fadar Shugaban Afirka ta Kudu da katse jawabinsa na gabatarwa da gangan, daga bidiyon bikin da ta watsa kai-tsaye.
Ya saka alamar tambaya kan me ya sa ba a cire jawabin jakadu 14 daga bidiyon ba, amma aka cire nasa.
Fani-Kayode shi ne na ƙarshe cikin waɗanda suka gabatar da jawabi, kuma jami’an Afirka ta Kudu sun ce tangarɗar na’ura ce ta haifar da katsewar.
Babu ‘katsewa da gangan’
Ita ma fadar shugaban ƙasar Afirka ta Kudu ta yi watsi da iƙirarin katsewa da gangan. Kakakin fadar shugaban ƙasar, Vincent Magwenya ya ce Ramaphosa ba shi da ikon katsalandan a hukuncin editocin kafar jaridar gwamnati kamar SABC.
Ita ma kafar yaɗa labaran ta fayyace cewa ɗaukar bidiyon shirin batu ne na daban daga shirye-shiryen watsa bikin fadar shugaban ƙasar.
Daga baya, fadar shugaban ƙasar ta wallafa cikakken bidiyon bikin a YouTube.
Amma lamarin ya haddasa muhawara da kuma rura taƙaddamar da ake yawan samu tsakanin ƙasashen biyu.
Haramtattun baƙin haure
A watannin Yuni da Yulin 2026, zanga-zangar adawa da ‘yan ƙasashen waje da kasuwancinsu a Afirka ta Kudu ta janyo Nijeriya ta kaddamar da kwashe ‘yanƙasarta kusan 1,500.
Sauran ƙasashen Afirka da dama sun ɗauki irin wannan mataki bayan tashin hankalin zanga-zangar ƙyamar baƙin.
Duk da taƙaddamar, Nijeriya da Afirka ta Kudu, biyu cikin ƙasashen Afirka mafiya ƙarfin tattalin arziƙi suna da alaƙar tarihi mai zurfi.
Nijeriya ta ba da babbar gudunmawa ga Afirka ta Kudu a fafutukarta ta yaƙi da mulkin danniya na apartheid, inda ta samar da tallafin kuɗaɗe da na diflomasiyya ga ƙungiyoyin neman ‘yanci.
Tun bayan ƙarshen apartheid a 1994, ƙasashen biyu sun gina alaƙar siyasa da tattalin arziƙi, inda Nijeriya ta zama babbar abokiyar cinikayyar Afirka ta Kudu a faɗin Afirka, duk da suna samun saɓani jifa-jifa.
A yanzu dai, gwamnatocin biyu sun jaddada aniyarsu ta girmama juna da ƙarfafa harkokin junansu.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: Others

