Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya ce Washington za ta tunkarar duk wani mummunan yanayi da ka iya tasowa, duk da cewa ba ta ga alamun wata babbar matsala a kusa ba, yayin da jerin matsalolin fasaha ke kawo cikas ga ayyukan wasu manyan hukumoni

Matsalolin fasaha sun katse ayyukan kamfanin Apple da manyan shafukan intanet a duniya

Kamfanin Apple ya sanar da samun matsalar katsewar ayyuka a sassa daban-daban na tsarinsa, lamarin da ya shafi kusan manyan shafukan intanet 200 kana ya kara yawan tsaiko na fasaha da suka kawo cikas ga ayyuka a Amurka da sauran sassan duniya.

A cewar shafin Apple da ke bayyana halin da tsarin ayyukansa ke ciki, an fuskanci jinkiri buɗe Asusun iCloud da tsarin shiga a ranar 17 ga watan Nuwanba.

Haka kuma, an samu katsewar sayen ayyukan AppleCare ta na'urorin kamfanin na wani dan lokaci, yayin da wasu masu amfani da Apple Business da Apple School Manager da kuma Schoolwork suma suka fuskanci tsaiko.

Matsalolin sun zo ne a daidai lokacin da ake samun rahotannin wani harin kutse na intanet da aka kai kan shafukan intanet na manyan kamfanoni da kungiyoyin kasa da kasa.

Daga cikin wadanda abin ya shafa akwai BBC, da CNN, da Zoom, da HSBC UAE, da Air France-KLM, da IKEA, da Salesforce da kuma GitLab.

A ranar Talata, kamfanin Google ya ce bai gano wata hujjoji da ke nuna cewa an samu katsewar ayyukan Gmail a faɗin duniya ba, duk da cewa dubban masu amfani da shafin sun bayar da rahoton fuskantar tsaiko yayin shiga asusunsu ko wajen duba sakonnin imel.

"A halin yanzu, ba mu samu wata hujja da ke nuna cewa an samu katsewar ayyukan Gmail a faɗin duniya ba. Kungiyoyinmu na sanya ido sosai kan yanayin ayyukanmu, ko da yake ana iya samun sabbin bayanai kan halin da suke ciki a kowane lokaci ta shafin Google Workspace Status Dashboard," a cewar wani mai magana dayawun Google.

Sanarwar ta biyo bayan korafe-korafe fiye da 2,800 da shafin Downdetector, mai bibiyar matsalolin ayyukan intanet ya samu kan matsalolin Gmail zuwa karfe 12 na rana agogon Gabashin Amurka (1700 GMT).

Vance ya bukaci a kasance cikin shirin ko-ta-kwana

Kazalika lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Donald Trump ke fuskantar tambayoyi kan irin karfin da tsarin fasahar sadarwar Amurka ke da shi na jure manyan matsaloli.

Da yake magana da tashar Fox News a ranar Litinin, Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya ce gwamnatin ba ta hasashen samun wata babbar matsala, amma tana cikin shirin ko-ta-kwana don tunkarar duk wani mummunan yanayi.

"Ba mu ga wata babbar matsala da ke tafe ba, amma dole ne a kasance cikin shirin tunkarar duk wani mummunan yanayi," in ji Vance ya.

Ya ce manufar gwamnatin ita ce "tabbatar da cewa mun hana faruwar mummunan yanayi, tare da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana."

Kalamansa sun biyo bayan jerin matsalolin da suka shafi fannin sufurin jiragen sama, da harkokin banki, da hanyoyin sadarwar hukumomin gwamnati da kuma manyan ayyukan Microsoft da kamfanoni ke amfani da su.

Tsaiko ga kamfanonin jiragen sama da bankuna

Kamfanin Microsoft ya fuskanci babbar matsalar katsewar ayyuka tsakanin ranakun 12 zuwa 14 ga watan Nuwamba, lamarin da ya shafi Outlook, da Teams da sauran ayyukan Microsoft 365 a faɗin duniya.

Kamfanin ya danganta tsaikon da wata matsalar kutsen fasahar software da ba a gano ta ba a watan Yuli. Ya ce lamarin ta ta’azzara ne sakamakon karuwar hanyoyin sadarwa da raguwar karfin rumbun bayanansa.

A ranar 13 ga watan Nuwamba, Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Amurka (FAA) ta ba da umarnin dakatar da tashin jiragen sama a faɗin kasar bayan da hanyar sadarwarta ta fuskanci tsaiko yayin aikin sabunta layukan sadarwa na fiber.

Matsalar ta dauki tsawon sa'o'i da dama, tare da haddasa soke dubban tashin jiragen sama.

Haka kuma an sake samun wata matsala a ranar Litinin, bayan da kamfanin jiragen sama na United Airlines ya sanar da matsalar fasaha da ta shafi tsarin da ma'aikatan jiragensa ke amfani da shi, ciki har da bayanan nauyin jiragen sama.

Matsalar ta dauki tsakanin mintuna 30 zuwa 90 kafin a shawo kanta, inda ta haddasa jinkirin tashin jiragen kafin a dawo da ayyukan yadda ya kamata.

Kamfanin United Airlines ya ce babu wata alama da ke nuna cewa matsalar na da alaka da harin kutse ta yanar gizo.

Manyan bankunan Amurka ma sun fuskanci matsalolin ayyuka a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Bankin Chase ya danganta matsalolin ayyukansa na intanet da wata matsala ta fasahar software, wadda ta kuma shafi wasu hada-hadar kudi da ke da alaka da wasu cibiyoyin kudi.

Bankin ya ce lamarin ba shi da alaka da harin kutse ta yanar gizo, kuma ba ya nuna cewa an samu matsala a dukkan tsarin hada-hadar kudi.

Matsalar ta shafi hanyoyin sadarwa na leken asirin Amurka

Rahotanni sun ce hanyar sadarwar sirri da Hukumar Tsaron Kasa ta Amurka (NSA) ke amfani da ita wajen sadarwa, wadda aka fi sani da NSANet, ta samu tangarda na dan wani lokaci a ranar 17 ga watan Nuwamba.

Wani jami'in Amurka ya danganta matsalar da aikin gyaran tsarin sadarwa da ake yi, ko da take ya ce , an ci gaba da gdanar da muhimman ayyukan hukumar.

Jami'an sun ce babu wata hujja da ke nuna cewa an kai harin kutse ta yanar gizo.

A wani rahoto na daban, kamfanin sa ido kan barazanar yanar gizo ta Google (Google's Threat Intelligence Group) ya yi gargadi a ranar Litinin cewa masu kutse suna kara amfani da na'urorin fasahar (AI) masu iya gudanar da ayyuka da kansu wajen kai hare-haren yanar gizo.

Kamfanin ya bayyana barazanar karuwar amfani da tsarin AI da ke iya gudanar da ayyuka ba tare da bukatar sa hannun dan Adam a kowane mataki ba a cikin rahotonsa mai taken "Agentic Threat Activity Crosses a Significant Threshold."

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: TRT World via AI

#