Gwamnatin ta kuma yi alƙawarin biyan basussukan alawus-alawus da sauran haƙƙoƙin ma’aikata da ba a biya ba, ciki har da bashin wani alawus na musamman da ya fara tun daga watan Mayun 2026. Za a biya bashin kashi-kashi cikin watanni uku.
Gwamnatin Nijeriya ta amince ta biya ma’aikatan gwamnatin tarayya alawus ɗin sufuri naira 70,000 duk wata har tsawon watanni shida, a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar da ta cim ma da Babbar Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasar, (NLC), domin rage raɗaɗin tsadar rayuwa, kamar yadda jami’ai suka bayyana ranar Laraba.
Yarjejeniyar ta nuna yadda matsalar hauhawar farashi ta zama batu mai matuƙar tasiri gabanin fatan Shugaba Bola Tinubu na a sake yin nasara a zaɓen watan Janairu. An yaba wa sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatinsa bisa inganta kuɗaɗen gwamnati, amma sun jefa miliyoyin ’yan Nijeriya cikin matsananciyar tsadar rayuwa wadda aka dade ba a fuskanci irin ta ba.
Kakakin Ma’aikatar Ƙwadago, Annah Daniel, ta ce ma’aikatan gwamnatin tarayya za su fara karɓar wannan kuɗi daga watan gobe.
Gwamnatin ta kuma yi alƙawarin biyan basussukan alawus-alawus da sauran haƙƙoƙin ma’aikata da ba a biya ba, ciki har da bashin wani alawus na musamman da ya fara tun daga watan Mayun 2026. Gwamnatin za ta biya wannan bashin kashi-kashi cikin watanni uku, inda za a fara biyan kuɗin a watan Nuwamba.
Yarjejeniyar ta kuma sake buɗe tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa. Bangarorin biyu sun amince da kafa kwamitin tattaunawa kan albashi nan take, duk da cewa har yanzu ba su cim ma matsaya kan lokacin da duk wani ƙarin albashi zai fara aiki ba.
Ma’aikatan lafiya za su karɓi biyan bashin alawus na watanni 19 da ba a biya su ba. Gwamnatin ta yi alƙawarin biyan duk bashin cikin watanni uku, daga watan Disamban 2026, matakin ya zama biyan ɗaya daga cikin buƙatun ƙungiyoyin ƙwadago da suka daɗe suna nema.
Sauran matakan da aka tattauna, ciki har da rage harajin da ma’aikata ke biya, za a miƙa su ga Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa domin nazari. A halin yanzu, ana tantance shawarwarin biyan alawus na haɗari ga ma’aikatan noma, tare da duba kuɗin da hakan zai ci.
Daniel ta ce bangarorin biyu sun amince su sake zama cikin wata guda domin duba irin ci-gaban da aka samu wajen aiwatar da waɗannan matakai.

