“A cikin shekara mai zuwa, Nijeriya za ta fara ƙera kayayyakin tsaro masu yawa domin biyan buƙatar cikin gida da kuma tallafa wa sauran ƙasashen Afirka,” in ji Janar Christopher Musa.

Nijeriya za ta fara ƙera makamai masu yawa nan da shekara ɗaya — Christopher Musa

Nijeriya za ta fara ƙera kayayyakin tsaro masu yawa nan da shekara ɗaya domin biyan buƙatar soji a cikin ƙasar da kuma fitar da kayayyakin zuwa sauran ƙasashen Afirka, kamar yadda Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya bayyana.

Musa ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata bayan ya halarci baje kolin tsaron Afirka na farko (AFRIDEX), wanda ya haɗa gwamnatocin Afirka da hukumomin soji da masu ƙera kayayyakin tsaro da masu samar da sabbin fasahohi a birnin Legas na Nijeriya.

Ya ce shirin fara ƙera makaman zai tallafa wa ƙoƙarin Nijeriya na rage dogaro kan shigowa da kayayyakin tsaro da kuma ƙarfafa ikon iya ƙera kayayyakin tsaro a cikin gida.

“Nan da shekara mai zuwa, Nijeriya za ta fara ƙera kayayyakin tsaro masu yawa domin iya biyan buƙatun cikin gida da kuma taimaka wa fitar da kayayyakin zuwa sauran ƙasashen Afirka,” kamar yadda Musa ya bayyana.

“Wannan wani muhimmin mataki ne zuwa samar da wata masana’antar tsaro mai cin gashin kanta, da ƙarfafa tsaron ƙasarmu da kuma saka Nijeriya a wani matsayi na mai ba da gudunmawa wajen ikon tsaro na Afirka,” in ji shi.

Ministan ya ce gwamnatin ƙasar tana son fara ƙera kayayyakin soji da makamai da sauran muhimman tsare-tsaren tsaro a cikin gida ta hanyar zuba jari da bayar da fasaha da bincike da haɗa ƙarfi da masu ƙera makamai na ƙasashen ƙetare.

Ya ce kamfanin ƙera kayayyakin tsaro na Nijeriya (DICON) na da muhimmanci a wannan ƙoƙari na faɗaɗa ikon iya ƙera kayayyaki a cikin gida da kuma samar da kayayyakin da sojojin Nijeriya ke buƙata.

A halin yanzu Nijeriya na shigowa ne da da yawa daga cikin kayayyakin soji daga ƙasashe irin su Turkiyya da Amurka da Faransa da Italiya da kuma China.

Musa ya ce AFRIDEX zai ba da damarmaki wa Nijeriya wajen zurfafa dangataka ta ƙasa da ƙasa da ta soji da musayar ƙwarewa da samar da hadin gwiwa wajen magance kalubale na tsaro a faɗin nahiyar.

Baje kolin ya haɗa da kayayyakin tsaro na ƙasa da sama da ruwa da kuma intanet, inda ya mayar da hankali kan haɗa buƙatun tsaro na Afirka da fasaha da ƙwarewa da ikon masana’antu da ake buƙata wajen magance su.

Ministan ya gode wa Shugaba Bola Tinubu kan tallafa wa shirye-shirye na ƙera kayayyakin tsaro na cikin gida kuma shirye-shiryen ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

 

 

#