Tawagar Benin ta yi ƙoƙarin ribatar buga wasan bankwana da tauraron ɗanƙwallon Argentina, amma a ƙarshe an bar su hannu-rabbana duk da yunƙurin nasu, a cewar kocinsu.
Kocin tawagar ƙasar Benin wadda ta fafata da Argentina a wasan sada-zumunta ranar Talata, ya koka kan abin da ya faru bayan wasan da aka buga a babban birnin Argentina.
Koci Gernot Rohr ya fusata game da yadda Lionel Messi, wanda ya buga wasansa na ƙarshe da tawagar Argentina, da kuma sauran taurarin Argentina suka yi na ƙin musayar jesi da ‘yanwasan Benin.
Cewar Rohr, hatta ɗaukar hoto ma an hana ‘yanwasansa yi da abokan wasansu, balle kuma da babban tauraron ƙwallo, Lionel Messi, wanda aka karrama a wasan.
Bayan wasan, Messi ya yi ritaya daga buga wa ƙasarsa yana mai shekaru 39, inda ya zura ƙwallo ɗaya ta bugun fenareti, ya kuma ba da tallafin ƙwallo biyu.
An tashi wasan Argentina tana da ci 3-0 kan Benin, abin da ya sanya Messi kammala wasa wa ƙasarsa cikin nasara da armashi.
Amma ga tawagar Benin kuwa, abin bai ƙare da daɗi ba, kasancewar bayan kammala wasan gabaɗaya an yi watsi da lamarin ‘yanwasansu.
Jiran minti 30
A cewar kocin, jami’an tsaro sun hana ‘yanwasansa gaisawa da ‘yanwasan Argentina, balle su yi musayar jesi kamar yadda aka saba gani a irin wannan wasa na biki.
Tawagar ta Benin ta yi ƙoƙarin ribatar wasan na bankwana da tauraron ɗanƙwallon, amma a ƙarshe an bar su hannu-rabbana duk da yunƙurin nasu, a cewar kocin.
"‘Yanwasana sun yi iya yinsu, amma ba su yi nasara ba. ‘Yanwasan Argentina sun ƙi ba wa ‘yanwasanmu komai, ko da ɗaukar hoto da Messi. Mun so mu yi musayar riguna, amma ba mu samu ko ɗaya ba. Sun ma hana mu shiga inda suke,” in ji Rohr.
Rohr ya ƙara da cewa, “‘Yanwasan Argentina ba su ba ‘yanwasanmu komai ba, ko da hoto da Messi. Mun so mu yi musayar jesi, amma ba mu samu komai ba”.
Rohr ya ce shi kansa ya yi jiran minti 30 kafin daga baya kocin Argentina, Lionel Scaloni ya ba shi wata ‘yar kyauta ta tsohuwar rigar da Messi ya saka a wani wasa, wadda shi kocin ya zo da ita.

