Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka FBI ta kama wasu mutane tara a Nijeriya da ke da alaka da zargin aikata laifuka a yanr gizo da ayyuka a cibiyoyin zamba.
Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka FBI ta kama wasu mutane tara a Nijeriya da ke da alaka da zargin aikata laifuka a yanr gizo da ayyuka a cibiyoyin zamba.
Daraktan FBI Kash Patel ya sanar da kama mutanen a ranar Litinin, yana mai cewa hukumomi sun kuma gano dala miliyan 11 a cikin asusun da za a iya saka wa takunkumi a cikin ƙasashe da dama.
A cikin wata sanarwa, Patel ya ce ana zargin waɗanda aka kama na gudanar da cibiyoyin zamba a Najeriya, suna kai hari ga waɗanda ba a san ko su waye ba, suna satar kuɗin da suka adana da kuma gudanar da ayyukan laifuka a ƙasashen duniya.
Ya ce aikin kamen, wanda aka yi wa laƙabi da ‘Operation Blackout’, an yi shi ne don wargaza hanyoyin sadarwa na yanar gizo na duniya da ake zargi da satar biliyoyin daloli daga Amurkawa.
A cewar Patel, frmakin ya kuma kai ga kwace na'urori guda 53.
Ya ce waɗanda ake zargin sun yi aiki ne bisa imanin cewa sun fi ƙarfin jami'an tsaro su gano inda suke, ya ƙara da cewa aikin ya nuna ƙoƙarin da ake yi na bin diddigin hanyoyin sadarwa na yanar gizo a kasashe.
Patel ya yaba wa hukumomin tsaro na Najeriya da abokan hulɗa a Landan saboda haɗin gwiwar da suka bayar a yayin kai farmakin.
FBI ba ta bayyana asalin waɗanda ake zargin ba ko kuma ta ba da cikakkun bayanai game da wuraren da ake zargin cibiyoyin zamba ne a Najeriya ba.
Kama mutanen ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin yaƙi da laifukan yanar gizo da zamba ta yanar gizo, waɗanda galibi ke haɗa hanyoyin sadarwa da ke aiki a ƙasashe da dama da kuma kai hari ga waɗanda abin ya shafa a wurare daban-daban.

