Tsohon shugaban Nijeriya ya nuna damuwa kan yadda wasu 'yansiyasa ke ƙara nuna rashin haƙuri ga masu ra'ayi mabambanta, tare da ƙin amincewa da haƙƙin sauran 'yantakara na fafatawa wajen neman madafun iko.
Tsohon shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, ya yi gargaɗin cewa ƙaruwar rashin haƙuri a siyasa, da tashe-tashen hankulan zaɓe da rarrabuwar kawuna tsakanin ƙabilu na iya yin barazana ga haɗin kai da zaman lafiyar ƙasar yayin da ake shirin babban zaɓen shekarar 2027.
Jonathan ya ce bai kamata ’yansiyasa su riƙa amfani da bambance-bambancen ƙabila da addini domin cim ma muradunsu na siyasa ba, yana mai gargaɗin cewa bai kamata neman mulki ya gurgunta zaman lafiya da haɗin kan al’umma ba.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wani taron zaman lafiya da tsaro na shekarar 2026 da Gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya a Abuja, mai taken, "Kare Amana da Ƙarfafa Haɗin Kan Al'umma a Yanayin Siyasa".
Tsohon shugaban ya nuna damuwa kan yadda wasu 'yansiyasa ke ƙara nuna rashin haƙuri ga masu ra'ayi mabambanta, tare da ƙin amincewa da haƙƙin sauran 'yantakara na fafatawa wajen neman madafun iko.
Ya kuma soki yadda ake ƙara amfani da matasa wajen haddasa tashin hankali a siyasa, yana mai gargaɗin cewa wasu jam'iyyun siyasa da ƙungiyoyin yaƙin neman zaɓe suna nuna halayen ƙungiyoyin asiri masu hamayya da juna.
"Ba wani abu da ya fi haɗarin da ke tattare da wanzuwar ƙasarmu gaba kamar tunzura rikicin ƙabilanci da gangan. Kada mu taɓa bari burin neman mulki ya lalata dangantakar da ke haɗa mu a matsayin al'umma da ƙasa ɗaya," in ji Jonathan.
Kazalika ya buƙaci shugabannin siyasa, da sarakunan gargajiya, da malaman addini da sauran masu tasiri a cikin al'umma da su fito fili su yi tir da kalamai da kuma ayyukan da za su iya haddasa rarrabuwar kawuna da raunana dimokuraɗiyya.
Kira ga zaɓen shugabanni nagari
Jonathan ya kuma buƙaci 'yan Nijeriya da su yi amfani da zaɓen 2027 wajen zaɓen shugabanni nagari a matakin tarayya da na jihohi, yana mai jaddada cewa ya kamata masu zaɓe su fifita ƙwarewa, gaskiya da kuma kishin ƙasa kan son zuciya ko kuma ƙabilanci.
Ya ce akwai buƙatar sake fasalin tsarin samar da shugabanni a Nijeriya domin tabbatar da cewa dimokuraɗiyya na samar da shugabannin da za su iya inganta haɗin kan ƙasa da kuma ci gaban al'umma.
Tsohon shugaban ya kuma nuna damuwa kan hukuncin kotuna masu matsayi ɗaya da ke cin karo da juna a kan rikice-rikicen siyasa.
Ya yi gargaɗin cewa irin waɗannan abubuwa na iya raunana aminci na al’umma ga ɓangaren shari'a, tare da sa wasu 'yan ƙasa su koma ɗaukar doka a hannunsu maimakon amfani da hanyoyin da kundin tsarin mulki ya tanada wajen warware saɓani.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: TRT Afrika Hausa

