Sauye-sauyen sun haɗa da cire shugabannin rundunar sojin ƙasa da na sama da kuma na ruwa.

Shugaban Benin ya sauya manyan hafsoshin soji bayan kusan shekara ɗaya da yunƙurin juyin mulki

Shugaban ƙasar Benin, Romuald Wadagni, ya yi garambawul ga manyan hafsoshin rundunar sojin ƙasar a ranar Laraba, bayan shafe kusan shekara guda da dakile yunƙurin juyin mulki a kasar.

A watan Disambar 2025 ne sojojin Benin suka dakile wani yunƙuri da wasu jami'an soja suka yi na hambarar da tsohon shugaban ƙasar, Patrice Talon, inda Nijeriya ta taimaka wajen dakile shirin.

Wannan sauyin shugabancin sojin na zuwa ne a daidai lokacin da Benin ke fuskantar ƙarin barazanar hare-haren 'yan ta'adda a yankunan arewacin ƙasar.

Wadagni, wanda ya hau kan mulki bayan lashe zaɓen watan Afrilu, ya naɗa Janar Abou Issa a matsayin sabon shugaban rundunar sojin ƙasar, inda zai maye gurbin Janar Fructeux Gbaguidi.

Ana sa ran Gbaguidi zai zama babban sakatare na dindindin na Majalisar Tsaro da Tsaron Ƙasa.

Haka kuma, an naɗa Kanal Andre Dokoui Fofo a matsayin shugaban rundunar sojin ƙasa, yayin da Kanal Herve Setondji Allotchenou zai jagoranci rundunar sojin sama na Benin.

Shi kuma Kyaftin Dossa Hounkpatin ne zai jagoranci rundunar sojin ruwa.

Wadagni, wanda ya shafe shekaru 10 yana riƙe da muƙamin ministan tattalin arzikin ƙasar, ya karɓi ragamar shugabancin Benin ne a lokacin da matsalar tsaro a arewacin ƙasar ke daga cikin manyan ƙalubalen da ke gabansa.

TRT Afrika — TRT Afrika

#