A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce ba za ta lamunci rashin haƙurin siyasa da kuma lalata kayan kamfen da gangan ba, tana mai gargaɗin cewa waɗanda suka aikata laifin da kuma waɗanda suka ɗauki nauyinsu za su fuskanci hukunci.

Rundunar ’yansandan Nijeriya ta gargaɗi ’yan siyasa kan lalata kayan kamfen gabanin zaɓen 2027

Rundunar ’Yansandan Nijeriya ta gargaɗi ’yan siyasa da magoya bayansu kan lalata fastoci da tutoci da allunan tallan kamfen na abokan hamayyarsu gabanin babban zaɓen 2027, tana mai cewa duk wanda aka samu da laifin zai fuskanci kama da gurfanarwa a gaban kotu.

A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce ba za ta lamunci rashin haƙurin siyasa da kuma lalata kayan kamfen da gangan ba, tana mai gargaɗin cewa waɗanda suka aikata laifin da kuma waɗanda suka ɗauki nauyinsu za su fuskanci hukunci.

Rundunar ta bayyana cewa cire fastocin wani ɗan takara ba bisa ƙa'ida ba ko lalata su laifi ne na ɓarnatar da dukiya, wanda doka ta tanadi hukunci a kansa, ciki har da sashe na 451 na dokar manyan laifuka (Criminal Code Act) da sashe na 326 na dokar hukunta manyan laifuka ta Penal Code.

Domin tabbatar da bin wannan umarni, Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya umarci kwamishinonin ’yan sanda a jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja da su ƙara sanya ido, gudanar da bincike kan rahotannin aikata irin waɗannan laifuka, tare da tabbatar da hukunta waɗanda aka samu da laifi.

Umarnin ya kuma shafi ’yan siyasa da sauran mutanen da ke ɗaukar nauyin aikata laifukan, ko ɗaukar mutane aiki, ko ba su kuɗi, ko ƙarfafa su su lalata kayan kamfen, muddin akwai hujjar da ke tabbatar da hannunsu a lamarin.

Rundunar ta jaddada cewa dukkan jam’iyyun siyasa da ’yan takara suna da haƙƙin samun kariya daidai wa daida a ƙarƙashin doka. Ta kuma yi gargaɗin cewa babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon yanke hukuncin ko kayan kamfen na wane ɗan takara ne za a bari a nuna ko kuma a lalata.

Saboda haka, rundunar ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da ’yan takara da magoya bayansu da su bi ƙa’idojin zaɓe, mutunta ra’ayoyin ’yan hamayya tare da gudanar da kamfen cikin lumana, yayin da harkokin siyasa ke ƙara ƙarfi gabanin zaɓen 2027.

TRT Afrika — TRT Afrika

#