Yankin kogin Nilu na da matukar muhimmanci ta fuskar harkokin soja da yanayin ƙasa, saboda yana da iyaka da ƙasashen Habasha da Sudan ta Kudu.
Rundunar sojojin Sudan ta ce ta dakile hare-haren dakarun RSF da ƙungiyar SPLM-N mai ƙawance da su a yankin kogin Nilu da ke kudu maso gabashin ƙasar, inda suka yi ‘‘asarar rayuka da kayan aikin yaƙi masu yawa.’’
A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a yammacin ranar Litinin, ta ce runduna ta 4 ta sojojin ƙasa ta ce dakarunta da sauran jami’an tsaro da ke taimaka musu sun hana maharan kutsawa sansanoninsu da ke Bakori, a ƙaramar hukumar Geissan, da kuma Sali, a ƙaramar hukumar Kurmuk.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana adadin mutanen da suka mutu ko irin kayan aikin yaƙi da aka lalata ba.
Kwamandan rundunar, Manjo Janar Ismail al-Tayeb Hussein, ya ce dakarunsa da sauran jami’an tsaro za su ci gaba da kare yankunan kogin Nilu tare da gudanar da ayyukan soji kan RSF da ƙawayenta.
Ƙaruwar faɗace-faɗace
Wannan arangama na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar faɗace-faɗace a yankin Kogin Nilu a ‘yan makonnin baya-bayan nan, inda RSF da SPLM-North suka yi ta kai kai hare-hare a wurare daban-daban.
A ranar 22 ga Oktoba, hukumomin Sudan sun sanar da cewa sojojin ƙasar sun sake kwace muhimmin yankin Bakori bayan fafatawa da ƙungiyoyin biyu.
Bakori na da tazarar kusan kilomita 70 daga kudu maso gabashin Damazin, babban birnin yankin. Haka kuma, akwai sansanin soji na Birged ta 13 ta rundunar sojojin ƙasa ta 4 a yankin.
Yayin da yankin Sali ke yankin kudu da Damazin, kusan kilomita 25 daga arewacin Kurmuk, kusa da iyakar ƙasar Habasha. Sojojin gwamnati sun ce sun dakile hare-hare da dama a yankin a cikin watan Oktoba.
Yankin Kogin Nilu na da matukar muhimmanci ta fuskar harkokin soja da yanayin ƙasa saboda yana da iyaka da Habasha da kuma Sudan ta Kudu.
Sudan na fama da yaƙi tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF tun watan Afrilun 2023, lamarin da ya ta’azzara matsalar jin kai, inda dubban mutane suka mutu, yayin da miliyoyin wasu suka rasa matsugunansu.
TRT Afrika — TRT Afrika

