Kakakin rundunar 'yansandan jihar, DSP Abayomi Jimoh, ne ya tabbatar da kamen a cikin wata sanarwa da ya fitar a Akure ranar Talata.

'Yansanda sun bankaɗo wurin buga jabun daloli, sun kama mutum ɗaya a Ondo

Rundunar 'yansandan Jihar Ondo da ke Nijeriya ta kama wani mutum tare da ƙwato buhuna uku na takardun dalar Amurka da ake zargin na jabu ne, bayan samamen da ta kai wani wurin da ake zargin ana buga kuɗaɗen jabun.

Samamen ya gudana ne a ƙauyen Kiniso, kusa da Ajue, a Ƙaramar Hukumar Odigbo ta jihar.

Kakakin rundunar 'yansandan jihar, DSP Abayomi Jimoh, ne ya tabbatar da kamen a cikin wata sanarwa da ya fitar a Akure ranar Talata.

Ya ce an fara binciken ne bayan wani mutum mai suna Yusuf Nasiru ya kai ƙara cewa wasu mutane biyu, Peter Desmond da Olami Toro, sun je shagonsa da ke Okitipupa a ranar 25 ga Oktoba, domin neman sauya musu dalar Amurka zuwa kuɗin Naira.

A cewar 'yansandan, Nasiru ya miƙa musu dala 6,000, wadda ta kai kimanin naira miliyan 8 da dubu 600.

Sai dai maimakon su ba shi kuɗin Naira, waɗanda ake zargin sun mayar masa da dalolin, suna masu cewa ba su da isassun kuɗaɗen da za su kammala cinikin, kafin su bar wurin.

Daga baya, Nasiru ya gano cewa dalolin jabun kuɗi ne, lamarin da ya sa ya kai ƙara ga 'yan sanda a ranar 28 ga Oktoba.

Jimoh ya ce jami'an rundunar 'yan sanda ta reshen Okitipupa sun fara bincike, inda suka yi amfani da bayanan sirri da kuma hanyoyin bin diddigi na fasaha wajen gano inda Desmond yake a ƙauyen Kiniso.

A ranar 29 ga Oktoba, jami'an 'yan sanda suka kai samame wurin da ake zargin ana amfani da shi wajen ƙera da buga jabun daloli domin damfarar jama'a.

An kama Desmond a yayin samamen, yayin da sauran mutanen da ke wurin suka tsere ta katangar harabar ginin.

'Yan sandan sun kuma kwato buhuna uku ɗauke da takardun dalar Amurka da ake zargin na jabu ne, tare da wani ƙaramin akwati na katako.

Kakakin rundunar ya ce wanda aka kama yana taimaka wa jami'an tsaro da bayanai masu amfani yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

TRT Afrika — TRT Afrika

#