Ƙasashen biyu sun musanta zarge-zargen tsoma baki a a cikin ƙasashen juna.

Ethiopia da Sudan sun rufe ofisoshin jakadancin juna bayan zarge-zargen tsoma baki a yaƙin basasa

Ethiopia da Sudan sun rufe ƙananan ofisoshin jakadancin juna kusa da kan iyakar ƙasashensu, kamar yadda jami’ai daga ƙasashen biyu suka bayyana ranar Laraba, lamarin da ya nuna ƙarin taɓarɓarewar dangantaka tsakaninsu kan zarge-zargen cewa ko wane ɓangaren na mara wa abokiyar gabar ɗayan baya.

Sudan tana zargi Ethiopia da tallafa wa rundunar RSF, yayin da Ethiopia ke zargin Sudan da goyon bayan ‘yantawaye a lardinta na Tigray da ke arewacin ƙasar.

Zarge-zargen da ramuwar zarge-zargen waɗanda dukkan ɓangarorin biyu suka musanta sun haddasa fargabar cewa yaƙe-yaƙen biyu za su iya shiga juna, lamarin da zai haddasa rikici mai ƙarin girma a yankin gabashin Afirka.

A ranar Lahadi, Gwamnatin Sudan ta ce ta kai ƙarar Ethiopia a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) da Kuma Kwamitin Tsaro da Zaman Lafiya na Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU). Addis Ababa ta musanta cewa tana mara wa RSF baya a yaƙin basasar Sudan.

Mayar da martani

Ethiopia ta rufe ƙaramin ofishin jakadancin Sudan ne a garin Assosa da ke kan iyaka kuma ta ba da umarni ga jami’an diflomasiyya shida su tafi cikin sa’o’i 48, kamar yadda wani babban jami’in Ethiopia ya shaida wa Reuters, ba tare da ba da wani dalili ga na ɗaukar matakin ba.

Bayan haka ne gwamnatin Sudan ta rufe ƙaramin ofishin jakadancin Ethiopia a birnin Gedaref na gabashin Sudan tare da korar jami’an diflomasiyya da ke aiki a wajen, kamar yadda jami’an Sudan biyu suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters.

Rikicin da ake a Sudan ya raba fiye da mutum miliyan 14 da gidajensu, in ji alƙalluman MƊD, kuma ya haddasa ɗaya daga cikin matsalolin jinƙai mafi muni a duniya tun lokacin da yaƙin ya ɓarke a watan Afrilun shekarar 2023.

Ethiopia ta zargi Sudan da Masar da Eritrea da goyon bayan ‘yan tawayen yankin Tigray. Sau dai duka ƙasashen uku sun musanta zargin.

TRT Afrika — TRT Afrika

#