Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 62 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 16,000, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 44,000 sun jikkata.
0230 GMT — Ana ci gaba da gwabza kazamin fada a kudancin Gaza yayin da Isra'ila ta mamaye yankin
Mayakan gwagwarmayar Hamas sun gwabza da sojojin mamaya na Isra'ila a tsakiyar babban birnin Gaza na kudancin kasar inda Isra'ila ke kyautata zaton akwai babban jagoran Hamas, yayin da Isra'ila ta matsa ƙaimi a yankin da ta yi wa ƙawanya.
Shaidu sun ce sojojin Isra'ila da tankunan yaƙi masu sulke da kuma manyan motocin yaƙi sun yi ta kai kawo a cikin Khan Yunus, lamarin da ya tilasta wa fararen hula da suka rasa matsugunansu sake tserewa, in ji shaidu.
Kungiyar Hamas ta ce da yammacin jiya Laraba a kafar Telegram cewa mayakanta na ci gaba da gwabza ƙazamin faɗa da sojojin da suka mamaye "dukkan yankuna suna kutsawa cikin Zirin Gaza", kamar yadda ta yi ikirarin cewa sun lalata motocin sojin Isra'ila biyu a Khan Yunis da Beit Lahia a arewacin yankin.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a cikin wata sanarwa ta faifan bidiyo ya ce sojojin Isra'ila suna kutsawa gidan shugaban Hamas a Gaza, Yahya Sinwar, inda mai magana da yawun Netanyahu ya ce Sinwar din na wani ginin karkashin kasa a yankin Khan Yunis.
Sai dai kungiyoyin agaji sun yi gargadin yaduwar yaƙin da Isra'ila ke yi a kudancin Zirin Gaza zai sa fararen hulan da suka tsere daga arewacin kasar, wadanda a yanzu yawancinsu sun shiga halin ha'u'la'i da rashin zaɓin inda za su.
"Muna cikin ɓacin rai, mun kai maƙura," in ji Amal Mahdi mazauniyar Khan Yunis. "Muna bukatar wanda zai nemo mana mafita domin mu fita daga cikin wannan hali."
2210 GMT — Isra'ila ta ce wa'adin mulkin Antonio Guterres "haɗari ne ga zaman lafiyar duniya"
Ministan Harkokin Wajen Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi Eli Cohen ya ce wa'adin shugaban Majalisar Dinkin Duniya hatsari ne ga zaman lafiyar duniya, yana mai cewa kiran da ya yi na tsagaita wuta a yaƙin da Isra'ila ke yi da Gaza da aka yi wa ƙawanya ya zama "goyon baya ga Hamas".
"Bukatarsa [Antonio Guterres] ta amfani da shafi na 99 da kuma kiran tsagaita wuta a Gaza ya ƙunshi goyon bayan ƙungiyar ta'addanci ta Hamas da kuma amincewa da kisan tsofaffi, da sace jarirai da fyaɗe ga mata," in ji Cohen, a wani saƙo da ya wallafa a shafin X.
Ya ƙara da cewa "duk wanda ke goyon bayan zaman lafiya a duniya dole ne ya goyi bayan ƙwato yankin Gaza daga hannun Hamas."