Rubio ya ce ba sabon abu ba ne shugabannin ƙasashe uku mafi ƙarfin makaman nukiliya a duniya su riƙa tattaunawa da juna.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce yiwuwar gudanar da taron shugabannin Amurka, Rasha da China zai zama “abu mai matuƙar amfani ga duniya”.
Rubio ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Indiya ranar Talata, inda ya ce Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna shirinsa na tattaunawa da shugabannin Rasha da China kan batutuwa kamar sarrafa makaman yaƙi.
Rubio ya ce ba sabon abu ba ne shugabannin ƙasashe uku mafi ƙarfin makaman nukiliya a duniya su riƙa tattaunawa da juna.
Ya kuma ƙi amincewa da ra’ayin cewa tattaunawar diflomasiyya na nufin bai wa wata ƙasa kyauta ko lada, yana mai cewa Trump ba ya ɗaukar tattaunawa da sauran ƙasashe a matsayin rangwame da ya yi musu.
Ya bayyana damar tattaunawa da ɓangaren da ake saɓani da shi a matsayin ginshiƙin diflomasiyya da sulhu.
Rubio ya amince cewa taro guda ba zai kawo ƙarshen saɓanin da ya daɗe tsakanin ƙasashen uku ba, amma ya jaddada muhimmancin ci gaba da tattaunawa.
Ya ce: “Ina ganin duniya ta fi samun tsaro idan shugabannin ƙasashen da suka mallaki manyan tarin makaman nukiliya a duniya suna tattaunawa da juna.”
Rubio ya kuma ce a baya China ta guji shiga tattaunawar sarrafa makaman nukiliya har sai tarin makaman nata ya kai matakin sauran manyan ƙasashe. Sai dai ya ce yana ganin abu ne mai kyau kasancewar Amurka na da shugaban da yake a shirye ya gwada wannan hanyar tattaunawa.
Jawabinsa ya biyo bayan furucin Trump a ranar Litinin, inda ya nuna buɗaɗɗiyar damar gudanar da tattaunawa tsakanin Amurka, Rasha da China. Trump ya ce babban abin da za a mayar da hankali a kai shi ne rage makaman nukiliya.
Batun yiwuwar taron ya fito ne bayan jaridar The Wall Street Journal ta ruwaito a ranar Lahadi cewa Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ba da shawarar gudanar da taron ƙasashen uku a wata mai zuwa domin tattauna hanyoyin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.
Mai magana da yawun fadar Kremlin, Dmitry Peskov, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa kan shawarar, yana mai amincewa cewa akwai yiwuwar gudanar da taron, duk da cewa har yanzu ba a cimma matsaya kan ajandar tattaunawar ba.
Duniya

