Kamfanonin tsaron Turkiyya na halartar taron Baje-Kolin Kayan Tsaro na Kasa da kasa na Afirka da ke gudana a Lagos, Nijeriya.

Kamfanonin Turkiyya na nuna kayayyakinsu a taron baje kolin kayan tsaro a Nijeriya

Kamfanonin tsaron Turkiyya na halartar bikin baje kolin tsaron kasa da kasa na Afirka na 2026 da ke gudana a Legas, Najeriya daga ranar Litinin, 26 ga Oktoba, domin nuna kwarewarsu ta fasaha.

Hukumar Masana'antun Tsaro ta Najeriya ce ta shirya taron na tsawon kwanaki hudu, wanda zai gudana daga Litinin zuwa Alhamis, domin inganta hadin gwiwa a fannin tsaro da musayar fasaha a fadin nahiyar.

Ana sa ran taron baje kolin zai jawo hankalin kamfanoni sama da 500 na duniya, sama da masu ziyara 20,000 da kuma wakilai sama da 100 na hukumomi.

Baje kolin ta hada fannoni tsaro kamar na ƙasa, sama, teku, sararin samaniya, da kuma tsaron yanar gizo.

Turkiyya ta samu cikakken wakilci

A filin baje kolin akwai kayan aikin soja da suka kama daga motocin yaƙi masu sulke, na'urorin harba manyan bindigogi da jiragen sama marasa matuki zuwa manyan na'urorin radar na zamani, guragen jiragen ruwa da hanyoyin sarrafa na'urori.

Taron na tsaro da aka gudanar a gefen bikin baje kolin ya karbi bakuncin masu jawabi na ƙasashen duniya sama da 200 a tarurruka 25 kan yaƙi da ta'addanci, tsaron teku, da kuma wanzar da zaman lafiya a yankuna.

Kamfanonin tsaron Turkiyya suna halartar bikin a ƙarƙashin wata rumfar ƙasa wadda Sakatariyar Masana'antun Tsaro ta Turkiyya ta tsara don samar da sabbin haɗin gwiwa.

Tawagar Turkiyya ta haɗa da kamfanonin Aselsan, Masana'antun Jiragen Sama na Turkiyya, Havelsan, MKE, STM, Skydagger, Med Marine, Isbir Generator da kuma Ipek Defense.

Fadada kawancen tsaro

Halartar Turkiyya wani bangare ne na kokarinta na fadada dangantaka a fannin tsaro a fadin nahiyar Afirka.

Har ila yau, wakilan kasashe daban-daban da suka hada da Amurka, China, Faransa, Jamus, Hadaddiyar Daular Larabawa, Brazil, India, Italiya, Poland, Saudiyya, da Koriya ta Kudu ma na halartar taron.

#