Yarjejeniyar na da zummar ƙarfafa alaƙar masana'antar tsaro tsakanin ƙasashen huɗu yayin da Qatar ƙe ƙoƙarin faɗaɗa ikonta na iya ƙera kayayyakin tsaro a cikin gida.
Ministan Tsaron Turkiyya Yasar Guler zai tafi Qatar domin halartar taron rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin kai ta masana’antar tsaro tsakanin ƙasashe huɗu, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Anadolu Agency ya ruwaito.
Ana sa rai Guler ya tashi zuwa Qatar ne ranar Talata, in ji wasu majiyoyi da kamfanin dillancin labaran ya ambato.
Turkiyya da Qatar da Pakistan da kuma Indonesia za su rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar Laraba.
A wani ɓangare na daban, nan ba da jimawa ba Qatar za ta ayyana shirye-shiryen kafa wata cibiyar samar da kayayyakin tsaro, kamar yadda ƙaramin ministan harkokin tsaron ƙasar Sheikh Saoud bin Abdulrahman Al Thani ya shaida wa wani Taron Tsaro na Duniya a Doha ranar Litinin.
Al Thani ya ce Qatar na aiki da abokan hulɗa na yanki da na ƙasa da ƙasa, ciki har da Amurka da Birtaniya da kuma Faransa, domin samar da ikon ƙara kayayyakin tsaro a cikin gida da kuma duba yiwuwar samun damarmaki na zuba jari a kamfanonin tsaro.
Ya kuma ce nan ba da jimawa ba Qatar za ta yi shelar wani sabon ƙawance na ƙarfafa iko kan makamai masu linzami da jirage mara matuƙa da hare-hare na intanet, ba tare da ba da ƙarin bayani ba.
Shelar na zuwa ne a cikin yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar kan Iran, wanda ya shafi fannin makamashin Qatar da kuma kasuwanci ta hanyar ruwa.
Qatar ta rufe da yawa daga cikin tashoshin iskar gas ɗinta a Ras Laffan jim kaɗan bayan fara yaƙin, yayin da taƙaita jigilar kayayyaki ta Mashigar Hormuz mai muhimmanci ya katse cinikayya ta duniya.
Turkiyya da Qatar sun ƙarfafa ƙawancensu a cikin ‘yan shekarun nan, suna masu faɗaɗa haɗin kai a harkokin tsaro da cinikayya da zuba jari. Ƙasashen biyu suna da wata cibiyar soji ta haɗin gwiwa a Doha kuma suna haɗa kai kan batutuwa na yanki.
A watan Oktoba na shekarar 2025, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta fahimtar juna kan haɗin kai na masana’antar tsaro a wani ɓangare na yarjejeniyoyi masu faɗi da zummar ƙarfafa dangantaka tsakaninsu.

