Ƙasashen Afirka bakwai sun nuna damuwa kan yadda ake ɗaukar 'ya'yansu don shiga yaƙin Rasha da Ukraine.

Akalla 'yan Uganda 27 sun halaka ko an yanke hukuncin sun halaka a yakin Rasha da Ukraine

Wata wasiƙa daga ofishin jakadancin Uganda a Moscow da ta aika wa ma’aikatar harkokin waje, ta ce ‘yan Uganda ashirin da bakwai da aka ɗauka sojin haya don yin yaƙi a rundunar sojin Rasha da ke Ukraine sun halaka, ko an ƙaddara halakarsu.

Wasiƙar, wadda Reuters ta gani ranar Alhamis, ta ba da sunayen ‘yan Uganda 11 da aka tabbatar da mutuwarsu, da kuma 16 da ba a samu gawarwakinsu ba, ciki har da fursunonin yaƙi.

Ofishin jakadancin Uganda ya ce ya samu bayanai daga ma’aikatar harkokin waje ta Rasha ta hanyar wata sanarwa 'ba ta baka ba'. Wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen Uganda ya tabbatar da sahihancin wasiƙar.

Rasha ta yi watsi da iƙirarin ɗaukar sojin haya
Ofishin jakadancin Rasha a Kampala bai ba da amsa kan lokaci ba, bayan aka tura masa tambayoyin jin ta bakinsa.

Rahotanni game da ‘yan Afirka da ake hilata zuwa Rasha da alƙawarin samun aiki, amma suke ƙarewa a bakin daga a Ukraine sun ƙaru. Hakan ya haifar da fushi tsakanin ƙasashen Kenya, Ghana da Afirka ta Kudu.

Ukraine ta faɗa a bara cewa fiye da mutum 1,400 ‘yan ƙasashen Afirka uku suna yaƙi tare rundunonin Rasha cikin iyakokin Ukraine.

Ta ce wasunsu an ɗauke su ne ta hanyar yaudara. Hukumomin Rasha sun musanta ana ɗaukar ‘yan Afirka ta haramtacciyar hanya don yin yaƙi a Ukraine.

#