Hana shiga da fita kusa da dandalin Place de la na Paris zai shafi dukkan mutane, tare da haramta zanga-zanga cikin dare a wasu unguwanni.

Faransa ta hana fita a sassan Paris yayin da zanga-zangar tsadar rayuwa ta haddasa tashin hankali

Bayan dubban mutane sun kwashe kwanaki da dama suna zanga-zanga inda a wasu lokuta suke haddasa tashin hankali, hukumomin Faransa sun sanya dokar hana fita ta dare daga ƙarfe 10 na dare zuwa ƙarfe 6 na safiya a kusa da dandalin Place de la Republique na Paris da kuma tituna da ke kewaye da yankin Les Halles, kamar yadda kafar watsa labaran Faransa BFMTV ta ruwaito ranar Litinin.

Hukumomi sun bayyana cewa hana fitar zai shafi dukkan mutane ne, ba yara kawai ba. Sun kuma bayyana cewa an hana zanga-zanga a wasu unguwannin Paris daga ƙarfe 8 na yamma zuwa ƙarfe 6 na safiya.

Taƙaita zirga-zirgar na zuwa ne yayin da hukumomi a faɗin Faransa ke ayyana dokokin hana fita da wasu matakai na tsaro bayan tashin hankali da fasa shaguna da wawason kayayyaki da aka yi yayin zanga-zangar da aka yi a faɗin ƙasar a ƙarshen mako kan tsadar rayuwa da farashin mai.

Hukumomin Faransa sun bayyana daga farkon ranar Litinin cewa za a ƙaƙaba dokar hana fita a garuruwa huɗu na arewaci da suka haɗa da Lille da Douai da Wattignies da Denain, na dare biyu, da yardar magajin gari na ko wanne daga cikin garuruwan.

Waɗannan matakan taƙaita zirga-zirgar za su yi aiki ne daga ƙarfe 8 na dare zuwa ƙarfe 6 na safiya.

Denain ta kuma fitar wata dokar taƙaita zirga-zirga ta daban daga ƙarfe 9 na dare zuwa ƙarfe 6 na safiya har zuwa ranar Lahadi 25 ga watan Oktoba.

Kimanin mutum 550,000 ne suka shiga zanga-zanga 110 a faɗin Faransa ranar Asabar, ciki har da mutum 110,000 a Paris, yayin da aka kama kimanin mutum 400 a fadin ƙasar, kamar yadda ministan cikin gida Laurent Nunez ya bayyana.

Firayim Minista Sebastien Lecornu ya bayyana ranar Litinin cewa ya nemi manyan jami’an gwamnati na yankuna (Prefects) su ayyana dokar taƙaita zriga-zirga bayan tashin hankalin.

Ya kuma ayyana wani muhimmin aiki na shari’a da wasu matakai na rashin aikin ga masana’auntu da tashin hankalin ya shafa.

Hukumomi sun kuma ayyana taƙaita zirga-zirga a Marseille.

#