Sojojin Koriya ta Kudu sun bayyana cewa Pyongyang ta harba makamai masu linzami zuwa Tekun Gabas wanda aka fi sani da Tekun Japan lamarin da ya sa aka aƙra sa ido da kuma ɗaukar matakan daƙile yiwuwar sake harba wasu makaman.
Koriya ta Kudu ta ce Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami da dama a cikin Tekun Japan.
"Da misalin ƙarfe 09:20 (0020 GMT) sojojinmu suka gano wasu makamai masu linzami da aka harba daga yankin Pyongyang zuwa Tekun Gabas," a cewar wata sanarwa da Hafsoshin Sojojin ƙasar suka fitar, tana mai nuni da Tekun Japan.
"Sojojinmu sun ƙara dabarun sa ido da kuma taka tsantsan kan yiwuwar ƙarin hare-hare," in ji sanarwar.
Hakan na zuwa ne bayan gwajin makami mai linzami da Pyongyang ta yi a farkon wannan watan wanda ta ce ya ƙunshi fasahar leƙen asiri.
Makami mai linzamin da aka harba a ranar 3 ga Oktoba, "yana iya canza saitin wurin da aka harba shi kuma yana amfani da ƙirƙirarriyar basira", kamar yadda Kim Yo Jong, 'yar'uwar shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, ta bayyana a lokacin
Bayan kwanaki Seoul ta sanar da nasarar gwajin wani makami mai linzaminta na farko mai ƙarfin gaske na (HGV) wanda ta ƙera a gida, wanda aka harba ta hanyar amfani da roka ko makamai masu linzami don saita inda ake son ya je.
Ofishin shugaban ƙasar Koriya ta Kudu ya ce makamin (HGV) na iya kai hari kan muhimman wurare a yankin Koriya, tare da ƙarfafa tsaron ƙasar.
Rikici tsakanin Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu ya ƙara tsananta bayan sojojin Koriya ta Kudu uku sun jikkata sakamakon fashewar nakiyoyi biyu a yankin da Seoul ke iko da shi wanda aka haramta gudanar da ayyukan soja (DMZ).
Yankin dai ya kasance tamkar shinge tsakanin ƙasashen biyu tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta shekarar 1953.
Wani bincike na haɗin gwiwa tsakanin Seoul da Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi zargin cewa Koriya ta Arewa ta dasa nakiyoyi a yankin fiye da shekara ɗaya da ta wuce, lamarin da Pyongyang ta musanta da kakkausar murya.

