‘Na ce Tamim, idan zai yiwu, a madadin Amurka, Rundunar Sojin Saman kasar, zan so na samu ikon aro ko amfani da jirginku na 747 a matsayin Jirgin Shugaban Kasa na dan wani lokaci, a yayin da muke jiran zuwan namu,’ in ji shugaban kasar Amurkan.
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a ranar Laraba cewa, da farko ya nemi Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, da ya ba Amurka aron jirgin sama kirar Boeing 747 domin amfani da shi na wucin gadi a matsayin jirgin shugaban kasa, amma sai shugaban na Qatar ya ba da shawarar kyautar da jirgin ga Washington maimakon bayar da shi a matsayin aro.
"Idan aka ba ka kyauta, ai za ka karba, ko ba haka ba?" in ji Trump yayin da yake jawabi ga taron jama'a a jihar Arizona. "Idan aka ba ka jirgin 747, abin da za ka ce kawai shi ne kalmomi biyu: 'na gode'."
Trump ya ce ya tuntubi Sheikh Tamim ne saboda jiragen saman da shugaban Amurka ke amfani da su a halin yanzu sun tsufa.
"Muna so mu karbi aron jirgin ne saboda jiragenmu sun shafe shekaru 35 suna aiki.
"Don haka na kira shugaban kasar Qatar—mutum ne mai matukar mutunci, mutum nagari, matashi, kuma kyakkyawa... sannan yana da kudi da yawa," in ji Trump.
“Na ce Tamim, idan zai yiwu, a madadin Amurka, Rundunar Sojin Saman kasar, zan so na samu ikon aro ko amfani da jirginku na 747 a matsayin Jirgin Shugaban Kasa na dan wani lokaci, a yayin da muke jiran zuwan namu.”
A cewar Trump, Sarkin ya ki amincewa da a ba shi jirgin a matsayin aro, sai dai ya ba da shawarar ya ba Amurka jirgin gaba ɗaya.
"Ya ce, 'A'a, a'a, a'a, a'a, a'a, a'a. Kai abokina ne. Ba zan bar ka ka are shi ka yi amfani da shi ba. Amma zan ba ka shi, a madadin Amurka. Ka ɗauke shi'," in ji Trump yana ba da labarin.
Ya ce ya karɓi jirgin a madadin Amurka.
Rundunar Sojan Sama ta Amurka ta sanya wa jirgin na Qatar suna 'VC-25B', kuma an yi niyyar amfani da shi a matsayin jirgin rikon-kwarya, yayin da sojojin ke jiran isowar sabbin jiragen shugaban kasa guda biyu kirar Boeing, waɗanda ake sa ran za su iso kasar a shekarar 2028.

