A cewar Channels Television, gwamnan ya ce tura jami’an aikin zai taimaka wajen ƙarfafa ayyukan tsaro, musamman a al’ummomin da ke cikin haɗari da yankunan dazuzzuka.

Kisan mutane a Filato: Mutfwang ya gargaɗi masu kai hare-hare, ya tura jami’ai 1,000 tsaron daji

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya gargaɗi waɗanda ke da hannu a kisan mutane da sauran hare-haren ta’addanci a jihar, yana mai cewa gwamnatinsa a shirye take ta yi amfani da dukkan ƙarfin yaƙi wajen tunkararsu.

Mutfwang ya yi wannan gargaɗin ne a birnin Jos yayin bikin kammala horas da jami’an tsaron dazuzzuka 1,000 ƙarƙashin shirin kafa rundunar tsaron dazuzzuka ta shugaban ƙasa, wanda gwamnatin tarayya da na jihohi ke gudanarwa tare.

A cewar Channels Television, gwamnan ya ce tura jami’an aikin zai taimaka wajen ƙarfafa ayyukan tsaro, musamman a al’ummomin da ke cikin haɗari da yankunan dazuzzuka.

Ya ƙi yarda da bayyana rikicin da ake fama da shi a Filato a matsayin rikicin manoma da makiyaya kawai, yana mai zargin cewa wasu ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai na kai hare-hare da gangan kan al’ummomi, kashe mutane da kuma ƙwace musu filaye.

Mutfwang ya kuma gargaɗi waɗanda ake zargin suna haɗa baki da maharan ko cin moriyar kisan mutane cewa kwanakinsu sun ƙare, yana mai cewa gwamnati na da bayanan sirri kan waɗanda ke da hannu a lamarin.

“Ba za mu taɓa kwatanta rayuwar saniya da ta ɗan’adam ba, haka kuma ba za mu kwatanta kuɗin hatsi da sauran kayan abinci da rayuwar ɗan’dam ba,” in ji gwamnan, yayin da yake Allah wadai da kashe mutane bisa dalilan satar shanu da lalata gonaki.

Ya buƙaci mazauna jihar da su taimaka wa hukumomin tsaro ta hanyar gaggauta kai rahoton duk wani motsi ko abin da suka zargi da aikata laifi. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa na ƙarfafa tattara bayanan sirri, tura jami’an kai ɗauki cikin gaggawa da kuma tsarin faɗakar da al’umma tun da wuri.

Da yake magana a madadin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, Salisu Muhammed ya ce za a tura sabbin jami’an nan take zuwa al’ummomin da ke cikin haɗari da yankunan dazuzzuka domin tallafa wa ayyukan tsaro da tattara bayanan sirri.

Mai kula da horas da jami’an ƙarƙashin shirin, Kyaftin ɗin Rundunar Sojin Ruwa, Uchendu Akalezi, ya ce jami’an 1,000 sun kammala horaswa mai zurfi a ƙarƙashin kulawar ƙwararrun malamai 25.

An kuma gudanar da kwaikwayon aikin ceto domin nuna irin shirin da jami’an suka yi na tunkarar ayyukan da za a tura su yi.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: Others

#