Kamfanin wasanni na mawaƙin Amurka, Jay-Z, wato Roc Nation Sports yana shirin tura ƙaramin yaron nan, Nevada Pierre zuwa Sifaniya a Disamba don samun horon ƙwallon ƙasa, cewar rahotanni.
Nevada Pierre, wani yaro Ba’amurke mai shekaru uku, wanda aka ce an umarce shi da ya bar gasar ƙwallon ƙafa ta yara saboda ƙwarewarsa ta zarce ta sauran ’yan wasan, ya samu goyon bayan mawaki Jay-Z, wanda ya yi tayin taimaka masa wajen bunƙasa harkar ƙwallonsa.
Rahotannin kafafen yaɗa labarai sun ce kamfanin Roc Nation Sports na Jay-Z na shirin aika Nevada zuwa Spain a watan Disamba domin taimaka masa wajen haɓaka ƙwarewarsa.
An kira ’yan sanda zuwa filin wasan ƙwallon ƙafa a ƙarshen makon da ya gabata, bayan iyayen yaran da Nevada ke karawa sun koka da cewa ƙwarewarsa ta sa wasan bai zama mai adalci ba, har ma ga yaran da suka kai shekaru biyar.
A yayin wasan da aka gudanar a Winter Park, jihar Florida, yaron ya riƙa sarrafa ƙwallo da ƙwarewa tare da zura ƙwallaye akai-akai. Rahotanni sun ce iyayen abokan karawarsa sun koka da cewa yana “riƙe ƙwallo na tsawon lokaci” kuma yana “ƙoƙarin nuna bajinta”.
Rikicin ya sa ’yan sanda suka raka iyalan Nevada daga filin wasan. Sai dai an mayar musu da kuɗin rajistar da suka biya gaba ɗaya.
Bayan faruwar lamarin, iyayen yaron, Martasia Griffin da Don Pierre, sun ƙaddamar da tara kuɗi domin taimaka masa wajen bunƙasa ƙwarewarsa ta ƙwallon ƙafa.
Kamfanin Roc Nation Sports ya nuna goyon bayansa ga yaron a shafinsa na Instagram, inda ya rubuta cewa: “Ka ci gaba da haskakawa, Nevada. Muna tare da kai!”
Nevada Pierre ya fara jan hankalin jama’a ne bayan da aka kira ’yan sanda a lokacin da yake wasa, bisa korafin cewa ya fi yaran da yake karawa ƙwarewa a ƙwallon ƙafa.

