An gabatar da kyaututtukan ne a bikin ba da lambar yabo ta Ballon d’Or karo na 70 da aka gudanar a zauren London Palladium, wanda shi ne karo na farko da aka gudanar da wannan babban bikin a babban birnin kasar Ingila.

Harry Kane ya zama Ingila na farko da ya lashe kyautar Ballon d’Or ta Maza a shekaru 25

Danwasan gaba na kungiyar Bayern Munich da Ingila, Harry Kane, ya lashe kyautar Ballon d’Or ta Maza ta shekarar 2026 a ranar Litinin, inda ya zama danwasa na farko dan kasar Ingila da ya karbi kyauta mafi daraja a fannin kwallon kafa a duniya tun bayan Michael Owen a shekarar 2001, yayin da ‘yar wasan Spain Alexia Putellas ta samu nata Ballon d’Or ta Mata karo na uku.

An gabatar da kyaututtukan ne a bikin ba da lambar yabo ta Ballon d’Or karo na 70 da aka gudanar a zauren London Palladium, wanda shi ne karo na farko da aka gudanar da wannan babban bikin a babban birnin kasar Ingila.

Kane, mai shekaru 33, ya lashe kyautar ne a karon farko bayan ya zura kwallaye 73 a wasanni 65 da ya buga wa Bayern Munich da Ingila a kakar wasa ta 2025/2026, ciki har da kwallaye 61 a wasanni 51 da ya buga wa kungiyar ta Jamus, wacce ta lashe kofi biyu a gida (gasar lig da kofin cikin gida).

Kyaftin din na Ingila ya kuma zura kwallaye shida a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026, inda ya taimaka wa kasarsa ta zo ta uku.

Danwasan gaba na Real Madrid da Faransa Kylian Mbappe ne ya zo na biyu a zaben Ballon d’Or na Maza, yayin da dan wasan Barcelona da Spain Lamine Yamal ya zo na uku.

Kane ya zama danwasa na biyar dan kasar Ingila da ya lashe kyautar, inda ya shiga ya sahun su  Stanley Matthews, Bobby Charlton, Kevin Keegan da kuma Owen, wanda shi ne dan Ingila na karshe da ya taba lashe kyautar a shekara ta 2001.

Ousmane Dembele na Paris Saint-Germain ne ya lashe kyautar a shekarar 2025.

A wani bangaren kuma, Putellas, mai shekaru 32, ta lashe kyautar Ballon d’Or ta Mata karo na uku biyo bayan nasarorin da ta samu a shekarar 2021 da 2022, inda ta yi daidai da tsohuwar abokiyar wasanta a Barcelona, Aitana Bonmati.

‘Yarwasan tsakiyar ta kasar Spain ta jagoranci Barcelona zuwa lashe kofuna hudu a jere a kakar wasa ta 2025-26, inda ta lashe La Liga F, Copa de la Reina, Super Cup ta Spain da Gasar Champions League ta Mata.

An kuma zabe ta a matsayin ‘yarwasan da ta fi kowa hazaka a Gasar Zakarun Turai sannan ta taimaka wa Spain lashe gasar Nations League ta Mata.

Putellas ta koma kungiyar London City Lionesses a watan Yuli bayan ta ci kofuna iri-iri a Barcelona.

Sauran wadanda suka lashe kyaututtuka su ne:

Dan wasan Barcelona da Spain, Lamine Yamal, ya lashe kyautar Kwararren Matashin Dan Wasa na Maza a karo na uku a jere, yayin da ‘yarwasan gaba ta Barcelona, Vicky Lopez, ta lashe kyautar ta mata a karo na biyu a jere.

Kocin Spain wanda ya lashe kofin duniya, Luis de la Fuente, an nada shi Kocin Maza na Shekara, yayin da Pere Romeu na Barcelona ya samu kyautar kocin mata.

Unai Simon na Athletic Bilbao ya lashe kyautar Gwarzon Gola na Maza na Shekara, yayin da Cata Coll ta Barcelona ta karbi kyautar a bangaren mata.

Kane na Bayern Munich ya kuma karbi kyautar Dan Wasan Gaba na Maza na Shekara biyo bayan kakar wasansa ta kwarewa, yayin da ‘yarwasan gaba ta Mexico, Charlyn Corral, ta zama ‘yarkasar Mexico ta farko da ta lashe kyautar ‘Yar Wasan Gaba ta Mata ta Shekara.

Barcelona ta samu kyautar Kungiyar Mata ta Shekara, yayin da Paris Saint-Germain (PSG) ta lashe kyautar kungiyar maza.

#