Matakan sun hada da cin kamfanin tarar kuɗi, ƙwace wasu rijiyoyin mai da yake gudanarwa da kuma sake bitar sharuɗɗan gudanar da ayyukan tafiyar da bututun mai da ya haɗa Nijar da Benin.

Nijar ta sanar da wasu matakai na hukunta kamfanin CNPC na China kan rikicin yarjejeniyar mai

Gwamnatin Nijar ta sanar da ɗaukar wasu matakai kan kamfanin mai na ƙasar China mallakar gwamnati, wato China National Petroleum Corporation (CNPC), bisa zargin rashin samun gagarumin ci gaba wajen cika alƙawuran da ke cikin yarjejeniyar haɗin gwiwar mai da suka ƙulla.

Matakan sun hada da cin kamfanin tarar kuɗi, ƙwace wasu rijiyoyin mai da yake gudanarwa da kuma sake bitar sharuɗɗan gudanar da ayyukan tafiyar da bututun mai da ya haɗa Nijar da Benin.

Sanarwar ta biyo bayan ƙarewar wa'adin watanni shida da kwanaki goma da aka bai wa kamfanin CNPC domin cika alƙawuran da ke cikin yarjejeniyar haɗin gwiwar mai da ɓangarorin biyu suka rattaɓa wa hannu.

An bayyana matakan ne a cikin wata sanarwa da aka karanta a yammacin ranar Asabar, ta hannun Bakary Yaou Sangaré, Ministan Harkokin Wajen Nijar, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin tattaunawa da abokan hulɗa a ɓangaren man fetur.

Kwamitin ya ce bayan tantance yadda aka aiwatar da yarjejeniyar a karshen wa'adin, ya gano cewa babu wani gagarumin ci gaba wajen cika alƙawuran da aka amince da su.

Nijar ta daɗe tana ƙoƙarin faɗaɗa aikin samar da man fetur da fitar da shi zuwa ƙasashen waje, inda kamfanin CNPC ke taka muhimmiyar rawa a ɓangaren man fetur na ƙasar.

Kamfanin na China ya taimaka wajen bunƙasa rijiyoyin man fetur na Nijar, tare da gudanar da bututun da ke kai ɗanyen mai daga Nijar zuwa Benin, wanda ke bai wa Nijar damar fitar da man fetur zuwa kasuwannin duniya ta tashar jiragen ruwa ta Benin.

Sabbin matakan da gwamnatin Nijar ta sanar na nuna yadda saɓani ke ƙara ƙamari tsakanin hukumomin ƙasar da kamfanin mai na China kan yadda ake aiwatar da yarjejeniyar haɗin gwiwarsu.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: Others

#