Zaɓen, wanda aka shirya shi domin nuna komawar ƙasar mulkin farar hula, bayan juyin mulkin da aka yi shekara guda daidai da ta gabata. Yanzu za a gudanar da zaɓen ne a ranar 26 ga Nuwamba, 2028.

Guinea-Bissau ta jinkirta zaɓen shugaban ƙasa da shekaru biyu

Mahukunta a ƙasar Guinea-Bissau sun sanar a ranar Alhamis cewa an dage zaɓen shugaban ƙasa da na ’yanmajalisar dokoki da aka shirya gudanarwa a watan gobe da shekara biyu.

An shirya gudanar da zaɓen ne a ranar 6 ga Disamba, domin ya zama alamar komawar ƙasar mulkin farar hula, bayan juyin mulkin da aka yi daidai shekara guda da ta gabata.

Sai dai wani umarni da shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya, Janar Horta N’Tam, ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa akwai ƙarancin “sharuɗɗan fasaha, da kayan aiki da kuɗaɗen da ake buƙata” domin gudanar da zaɓen.

Yanzu haka, za a gudanar da zaɓen ne a ranar 26 ga Nuwamba, 2028.

N’Tam ya ce akwai buƙatar “tabbatar da bin doka, da gaskiya, da bai wa kowa dama da kuma sahihancin tsarin zaɓe”.

Ya ƙara da cewa akwai kuma buƙatar “ƙarfafa ƙananan hukumomi” ta hanyar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a karon farko a tarihin ƙasar.

Sojoji sun ƙwace mulki a Guinea-Bissau kwanaki kaɗan bayan zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 23 ga Nuwamba, 2025. An hambarar da tsohon shugaban ƙasar, Umaro Sissoco Embalo, sannan aka dakatar da tsarin zaɓe.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: AFP (Wire)

#