Shugaban ƙasar ya ce za a ci gaba da tabbatar da nasarorin da sojoji suka samu wajen samar da tsaro a jihar Borno da sauran sassan Arewa maso Gabas, tare da mayar da su ginshiƙin farfaɗo da tattalin arzikin yankin.
Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na tabbatar da ɗorewar zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa maso Gabashin ƙasar, inda ya umarci hukumomin tsaro da su ƙara tsananta hare-hare kan ’yan ta’addan da ke tserewa.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin ziyarar da ya kai Maiduguri, babban birnin jihar Borno, inda ya halarci wani gangamin siyasa gabanin yunƙurinsa na sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Shugaban ƙasar ya ce za a ci gaba da tabbatar da nasarorin da sojoji suka samu wajen samar da tsaro a jihar Borno da sauran sassan Arewa maso Gabas, tare da mayar da su ginshiƙin farfaɗo da tattalin arzikin yankin, kamar yadda sanarwar da Bayo Onanuga jam’iyyar ta wallafa a shafinta na
Ya yaba wa Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, kan ƙoƙarin da yake yi na dawo da zaman lafiya da sake gina tattalin arzikin jihar, yana mai cewa inganta tsaro ya samar da damar aiwatar da ayyukan ci gaba.
Tinubu ya kuma yi kira ga ’yan ta’addan da ke ci gaba da ayyukansu a yankin da su miƙa wuya tare da ajiye makamansu, yayin da ya tabbatar wa jami’an soji cewa gwamnati za ta ci gaba da ba da muhimmanci ga jin daɗinsu da na iyalansu.
Dangane da sace ɗaliban makarantar Askira-Uba da ke jihar Borno, shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa za ta ƙara ƙaimi wajen tattara bayanan sirri domin ceto su.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa sojoji za su yi nasarar kuɓutar da yaran ta hanyar ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro da amfani da bayanan sirri.
Tinubu ya danganta nasarorin da aka samu a yankin da haɗin gwiwar gwamnatocin jihohi, da shugabannin al'umma, da mazauna yankin da kuma hukumomin tsaro na gwamnatin tarayya.
Ya kuma yi tsokaci kan jarin da aka zuba a fannonin ilimi, da kiwon lafiya da ababen more rayuwa cikin shekaru uku da suka gabata, inda ya ambaci ƙaddamar da masaukin mata masu yi wa ƙasa hidima na NYSC da Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa ta Borno da ke Maiduguri.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi kira ga mazauna yankin Arewa maso Gabas da su goyi bayan ƙoƙarin Tinubu na sake neman wa'adi na biyu, yana mai cewa gwamnatin ta aiwatar da ayyukan ci gaba a jihohin Borno, da Bauchi, da Taraba da kuma Adamawa.
Shettima ya kuma soki burin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, wanda yake takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, inda ya nuna shakku kan ikonsa na samar da ingantaccen shugabanci a matakin ƙasa.
Kazalika, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya yaba wa Tinubu kan tallafin da ya bayar ga jihar, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen inganta tsaro da farfaɗo da tattalin arzikinta.
Zulum ya ambaci zuba jari a jami’o’i, da hanyoyi da sauran ababen more rayuwa, ciki har da hanyar Biu zuwa Maiduguri, a matsayin misalan tallafin gwamnatin tarayya.
Ya kuma yaba wa Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas (NEDC), musamman kan samar da motocin bas masu amfani da lantarki guda 10,000 ga yankin.
An gudanar da gangamin ne tare da halartar shugabanni da magoya bayan jam’iyyar APC, inda Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya miƙa tutocin jam’iyyar ga ɗan takararta na gwamna a jihar Borno da sauran ’yan takara gabanin zaɓe mai zuwa.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: TRT Afrika Hausa

