An haifi Edochie ne ranar 7 ga watan Maris na shekarar 1947, a Zaria, Jihar Kaduna, kuma ya kasance ɗan asalin ƙabilar Igbo. Ya halarci makarantun Firamare na St. Patrick da St. James a Zaria.
Fitaccen Jarumin fina-finan Nijeriya na Nollywood, kuma tsohon ɗanjarida Pete Edochie ya rasu yan ada shekara 79 da haihuwa, kamar yadda iyalisan suka bayyana ranar Laraba.
Wata sanarwar da ɗan marigaryin, Leo Pete Edochie, ya fitar a madadin iyalinsa, ta ce ɗanwasan kwaikwayon ya rasu ne da misalin ƙarfe 12:30 kafin asubahin ranar 25 ga watan Nuwamban 2026 a Enugu bayan ya ɗauki lokaci yana fama da kansar mafitsara.
Iyalin sun bayyana marigayin a matsayin “mijinmu da babanmu da ɗanuwanmu da muke so”.
“Da cikakken baƙin ciki da kuma zuƙata da suka miƙa wuya ga muradin Allah maɗaukaki, muna shelar rasuwar mijinmu da babanmu da ɗanuwanmu..., Cif Dr Pete EDOCHIE.., tsohon ma’akacin rediyo da talabijin da kuma fitaccen ɗanwasan kwaikwayo,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Marigayin wanda ɗan asalin Akamnato Ifite Nteje ne a Jihar Anambra state, ya rasu ya bar matarsa Josephine Edochie da yara da ‘yanuwa da yawa.
Kazalika iyalinsa sun bayyana cewa za a fitar da shirin jana’iazarsa sannun a hankali.
“Yayin da muke jimamin wannan rashin mai raɗaɗi, muna addura cewa Allah madaukaki zai bai wa ransa hutu mai ɗorewa da da kuma bai wa iyalisan haƙurin jure wannan babban rashin,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
“Alla Ya kasance tare da mu a wannan lokaci mai matuƙar wahalar,” in ji sanarwar.
An haifi Edochie ne ranar 7 ga watan Maris na shekarar 1947, a Zaria, Jihar Kaduna, kuma ya kasance ɗan asalin ƙabilar Igbo. Ya halarci makarantun Firamare na St. Patrick da St. James a Zaria kafin ya wuce makarantar St. John’s College don karatun sakandare. Daga baya ya yi karatu a makarantar Aikin Jarida da Talabaijin a Ingila.
Shauƙin Edochie ga wasan kwaikwayo ya bayyana ne tun yana yaro, yayin da ayek ɗalibi a makaranatar sakandaren St. John College a Kaduna. A shekarar 1962, a lokacin da ayke ɗan shekara 15, ya kasan cikin ‘yan wasan kwaikwayon da suka yi wasan ‘The Merchant of Venice’ na William Shakespeare a kan dandali.
A shekarar 1967, Edochie ya fara aiki a gidan rediyo da talabijin, inda ya samu matsayin ƙaramin mataimakin mai tsara shirye-shirye da gidan Watsa Labaran Gabashin Nijeriya (ENBS), ma’aikatar da za ta koma Gidan Watsa labaran Jihar Anambara (ABS).
Ya shafe shekaru yana ƙara girma har zuwa lokacin da ya kai matakin darakta. Ya yi aiki a matsayin daraktan tsara shirye-shirye da mataimakin manajin darakata kuma a wasu lokuta ya yi aiki a matsayin muƙaddashin manajin darakta. Aikinsa a ABS ya ƙre ne a lokacin da gwamnatin ta zaaɓi shigar da siyasa cikin ayyukan tashar FM ɗinsa, wani matakin da ya sa aka buƙci dukkan shugabannin digan watsa labaran, ciki har da Edochie, su ja gefe.
Duk da cewa a da shi aka tsayar don ya zaman Manajin Darakta na gaba, ya bar gidan kuma ya shiga cikin harkar fina-finai.
Kafin wannan sauyin, ya riga ya samu damar aikin fim ɗinsa na farko a matsayin jarumi Okonkwo wasaj talabijin na da aka yi kan littafin ‘Things Fall Apart,’ wanda aka yi a gidan atalabijin na Nijeirya (NTA) a shekarar 1987.
Edochie ya kasance ɗaya daga cikin ‘yanwasan kwaikwayon da suka fi fice a Nijeriya, inda ya yi fice da yadda yake jan hankali a fina-finai da kuma rawar da ya taka a fagen fina-finan Nollywood.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: YulEdochie

