Yayin da Real Madrid ta doke PSV Eindhoven da ci 5-1, kana Arsenal da Manchester City suka tashi kunnen doki da Borussia Dortmund da Napoli, duka bi da bi.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray ta Turkiyya ta doke Aston Villa ta Ingila da ci 1-0 a gidanta, a wasan zagaye na biyar na matakin rukuni na gasar Zakarun Turai ta UEFA, inda ta samu nasarar lashe wasanni uku a jere a gasar.
An tashi wasan zagayen farko babu ci a filin wasa na RAMS Park da ke Istanbul, inda babu wata ƙungiya da ta samu damar zura kwallo a ragar abokiyar hamayyarta.
Galatasaray ta yi canje-canjen ‘yanwasa a zagaye na biyu, inda ta shigar da ɗan wasan gaban ƙungiyar, Deniz Gül, a mintuna na 62, sannan ta shigar da Gabriel Sara a mintunu na 74 domin neman hanyar zura samun ƙwallo.
Canje-canjen sun haifar da sakamako a minti na 77, lokacin da Sara ya yi wani bugun kusurwa daga gefen dama, wanda ya bai wa Wilfried Singo damar karkatar da ƙwallon da kai zuwa kusa da raga.
Ƙwallon ya shafi jikin ɗan wasan Aston Villa, Nicolas Jackson, kafin Deniz Gül ya yi saurin buga shi da ka zuwa cikin raga daga kusa, lamarin da ya bai wa Galatasaray damar cin ƙwallo.
Aston Villa ta kasa rama ƙwallon a sauran lokacin wasan, yayin da Galatasaray ta samu maki uku.
Nasarar ta kara yawan makin Galatasaray zuwa tara bayan wasanni biyar, daidai da na Aston Villa, wadda ita ma take da maki tara.
Galatasaray za ta ziyarci AEK Athens a ranar 8 ga Disamba, yayin da Aston Villa za ta karɓi bakuncin Paris Saint-Germain a ranar, a zagaye na shida na gasar.
Sauran sakamakon wasannin
A bagare guda kuma, Real Madrid ta kasar Sifaniya ta yi nasarar dawowa da karfi inda ta doke PSV Eindhoven da ci 5-1, kuma ta ci gaba da samun nasara a dukkan wasanninta a gasar.
Arsenal ta tashi kunnen doki 1-1 da Borussia Dortmund, a wasan da kocin Arsenal, Mikel Arteta, ya kare ɗan wasansa Viktor Gyökeres kan watsar da damar da ya samu na cin ƙwallaye.
Haka kuma a nata ɓangaren, Manchester City ta tsira daga shan kaye bayan da ɗanwasanta Rayan Cherki ya zura ƙwallon farko a mintunan ƙarshe, inda ta tashi 2-2 da Napoli. Sai dai kunnen dokin bai kawo ƙarshen matsalolin da ƙungiyar ke fuskanta a ciki da wajen filin wasa ba.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: Anadolu Agency (Wire)

